Nasarar Buhari alama ce ta nasarar Dimokuradiya - Mijinyawa

Nasarar Buhari alama ce ta nasarar Dimokuradiya - Mijinyawa

A jiya Talata, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

Kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Alhaji Kabiru Mijinyawa, ya yi jinjina tare da bayyana farin cikin sa kwarai da aniyya dangane da sake samun nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin babban zaben kasa da aka gudanar a makon da ya gabata.

Nasarar Buhari alama ce ta nasarar Dimokuradiya - Mijinyawa
Nasarar Buhari alama ce ta nasarar Dimokuradiya - Mijinyawa
Asali: UGC

Alhaji Mijinyawa ya ce, nasarar shugaban kasa Buhari ta samun tazarce akan kujerar sa ta mulki, alama ce ta tabbatuwar kasar nan da kuma al'ummar ta akan tafarki na ci gaba da sharbar romon dimokuradiya maras yankewa.

Jagoran Majalisar jihar Adamawa da ta kasance Mahaifa ga Atiku, ya yi wannan furuci biyo bayan sanarwar shugaban kasa hukumar zabe ta kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, da ya tabbatar da nasarar shugaban kasa Buhari da misalin karfe 3.00 a daren yau na Laraba Talata, 27 ga watan Fabrairu.

KARANTA KUMA: Abubuwa 10 game da Buhari bayan samun nasara

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya lallasa sauran 'yan takarar kujerar shugaban kasa 72 yayin da lashe gamayyar kuri'u 15,191,847 daga dukkanin jihohin 36 da ke fadin kasar nan da kuma babban birnin tarayya na Abuja.

Alhaji Majiya ya kara da cewa, nasarar shugaban kasa Buhari yayin babban zabe kasa manuniya ce ta cikar buri da kuma tabbatar muradi na al'ummar kasar nan da kishin kasa ya mamaye zukatan su

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel