Buhari ya sha gaban Atiku Abubakar a halin da ake ciki a Gombe
Dan takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari ne ke kan gaba a iya sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar a jahar Gombe, inda Atiku ke binsa a baya.
Legit.ng ta ruwaito zuwa yanzu an sanar da sakamakon zabe na kananan hukumomi guda tara cikin kananan hukumomin jahar guda goma sha daya, inda a yanzu Buhari ke jan gora a kananan hukumomi guda bakwai, Atiku kuma yana da biyu.
KU KARANTA: Albarkacin kaza: Dan yayar Buhari ya yi biji biji da jam’iyyar PDP a takarar dan majalisa
Kafatanin kuri’un da Buhari ya samu a iya kananan hukumomi guda taran da aka sanar da sakamakonsu shine dubu dari uku da daya da dari shida da saba’in da bakwai, yayin da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u dubu dari da goma da dari biyu da shirin da tara, 110, 229.
Sauran kananan hukumomi biyu da ba’a sanar da sakamakonsu ba sun hada da Akko da Funakaye, amma ga jerin sakamakon kananan hukumomin da aka sanar guda tara:
Balanga:APC – 29, 697, PDP- 14, 614
Billiri: APC – 15, 331, PDP – 21, 328
Dukku: APC – 32, 010, PDP – 7, 437
Gombe: APC – 86, 162, PDP – 7, 634
Kwami: APC – 36, 317, PDP – 6, 614
Nafada: APC – 15, 417, PDP – 5, 792
Kaltungo: APC – 20, 944, PDP – 20, 733
Shomgom: APC – 9, 642, PDP – 12, 871
Yamaltu Deba: APC 56, 157, PDP – 13, 208
A wani labarin kuma, gwamnan jahar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ya fadi warwas a kokarinsa na haurawa majalisar dattawa a inuwar jam'iyyar PDP, inda dan takarar APC Saidu Alkali ya lallasashi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng