Sakamako: Duk da an sake kirga kuri’u, Atiku ya lallasa Buhari a fadar shugaban kasa

Sakamako: Duk da an sake kirga kuri’u, Atiku ya lallasa Buhari a fadar shugaban kasa

Jami’an hukumar zabe mai zaman ta kasa (INEC) sun sake kidaya kuri’un zabe da aka kada a fadar shugaban kasa bayan kirga na farko da su ka yi a jiya wanda ya nuna cewar dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ne a gaba da shugaba Buhari.

A kidayar da INEC ta yi, sakamako ya nuna cewar Atiku ya shiga gaban Buhari da kuri’u 17.

A yayin da shugab Buhari ke da kuri’u 1,013, Atiku ya samu kuri’u 1,030

Sakamako: Duk da an sake kirga kuri’u, Atiku ya lallasa Buhari a fadar shugaban kasa
Atiku da Buhari
Asali: Depositphotos

Zaben na jiya, Asabar, dai ya fi jan hankali ne a matakin kujerar shugaban kasa tsakanin manyn ‘yan takara; shugaba Buhari a jam’iyyar APC da babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Zabe: Sule Lamido ya fita kunyar PDP da Atiku a mazabar sa

Manema labarai da ‘yn jarida sun fi mayar da hankali a kan sakamakon mazabun manyan ‘yan siyasa da ke goyon bayan ‘yan takarar biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel