2019: Buhari ya yi nasara a mazabar Lamidon Adamawa

2019: Buhari ya yi nasara a mazabar Lamidon Adamawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yiwa Wazirin Adamawa kuma dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, mugunyar kayi a rumfar zabe ta mazabar fadar Lamidon Adamawa da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.

Alkalin zaben, Idris Yunusa, yayin bayyana wannan sanarwa ya zayyana yadda shugaba Buhari dan takara na jam'iyyar APC ya lashe kuri'u 228 yayin da Atiku na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 138 a rumfar zabe ta 10 dake unguwar Mbamoi.

2019: Buhari ya yi nasara a mazabar Lamidon Adamawa
2019: Buhari ya yi nasara a mazabar Lamidon Adamawa
Asali: UGC

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito, baya ga samun nasara a mazabar sa ta Sarkin Yara da ke garin Daura a jihar Katsina, shugaban kasa Buhari ya kuma lallasa Atiku a mazabar sa ta unguwar Ajiya da ke birnin Yola.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Atiku ya gaza kawo akwatin sa yayin da shugaba Buhari ya lallasa shi da kuri'u 186, inda shi kuma ya tashi da kuri'u 167 kacal.

KARANTA KUMA: Ba bu ruwan ku da ra'ayin siyasa - Shugaban hafsin sojin sama ya gargadi Dakaru

Mun samu cewa, shugaban kasa Buhari ya yi nasara a mazabar fadar gwamnatin jihar Benuwe da ke birnin Makurdi yayin babban zaben kasa da aka gudanar a jiya Asabar, 23, ga watan Fabrairun 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel