Mace kamar maza: 'Yar sanda ta hana satar akwatin zabe a Ogun (Bidiyo)

Mace kamar maza: 'Yar sanda ta hana satar akwatin zabe a Ogun (Bidiyo)

Wata jami'ar 'yan sandan Najeriya tayi jarumta inda ta taka wa wani matashi birki a yayin da ya yi yunkurin sace akwatin kuri'a na zabe a ward 5 da ke Odo Oba a Abeokuta ta Kudu na jihar Ogun.

Matashin ya yiwa abokansa barazanar cewa zai iya sace akwatin zaben ne amma a yayin da ya yi yunkurin sacewar sai 'yar sandan tayi wuf da cafke shi tare da akwatin zaben.

A cewar Sahara Reporters, tuni an mika matashin ga jami'an 'yan sandan farar hula ta DSS kuma sunyi gaba dashi.

Kalli bidiyon a kasa:

KU KARANTA: Kai-tsaye: Yadda zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya ke gudana a Sokoto, Jigawa da Kebbi

Kafin zabe dai shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa duk wanda ya yi yunkurin sace akwatin zabe toh a bakin ransa.

"Ina gargadin duk wanda ya ke tunanin yana da iko a garinsa har zai sanya 'yan daba su sace akwatin zabe ko kawo cikas a zabe, duk wanda ya aikata hakan toh a bakin ransa," inji Buhari.

Mutane da dama sun nuna rashin jin dadinsu a game da kalaman na shugaban kasa.

Sai dai hukumar INEC tayi karin haske inda ta ce duk wanda aka samu ya karya wata dokar zabe za ayi amfani da dokokin hukumar zabe ne wurin hukunta shi.

Shima sufeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya ce za a hukunta masu satar akwatin zabe kamar yadda doka ta tanada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel