Hanyoyi 7 da mutum zai yi ba tare da ya tara wa kansa gajiya ba

Hanyoyi 7 da mutum zai yi ba tare da ya tara wa kansa gajiya ba

Ranar zabe rana ce mai matukar muhimmanci a wurin masu kada kuri'a inda za su samu daman fita su zabi wanda suke ra'ayi domin ya jagorance su a shekaru 4 masu zuwa.

Saboda muhimmancin ranar ya sanya Legit.ng ta kawo muku wasu hanyoyi da zaku bi domin samun nasarar kada kuri'unku cikin sauki.

Kai-tsaye: Yadda zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya ke gudana a Kebbi

Kai-tsaye: Yadda zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya ke gudana a Kebbi
Source: UGC

1. Tafiya wurin zabe a kan lokaci

Zuwa rumfar zabe a kan lokaci zai bawa mutum damar samun layi kusa da rumfar kada kuri'a kuma a kauce wa ture-ture da sauransu.

2. Saka tufafi da suka dace da yanayi

Akwai yiwuwar mai kada kuri'a zai kwashe sa'o'i masu yawa kafin ya yi zabe hakan yasa yana da muhimmanci mutum ya saka tufafi masu saukin sha'ani tare da takalma da ba za su takurawa mutum ba.

DUBA WANNAN: Zabe: Shugaban PDP na jihar Yobe ya koma APC, ya yi mubaya'a ga Buhari

3. Tafiya wurin zabe da maganinka

Akwai wasu mutane da ke fama da ciwo da ke bukatar amfani da magunguna a kan kari misali ciwon Asthma, yana da kyau mutum ya tafi da maganinsa wurin zaben saboda ko ta kwana.

4. Rike ruwan sha ko wani abin sha

A rana irin ta zabe mutum zai kwashe lokaci mai tsawo yana tsaye kuma idan lokacin zafi ne kishin ruwa yana yawan damun mutane, yana d kyau mutum ya tafi da ruwa ko wani abin sha da zai rika jika makogoro.

5. Ci abinci kafin ka tafi wurin zabe

Yana da muhimmanci mutum ya ci abinci mai kyau kafin ya tafi wurin kada kuri'a saboda akwai yiwuwar za a dade kuma ana tsaye ne. Mutum yana iya tafiya da kayan marmari idan yana da hali.

6. Takatsantsan da kayayakin ka

Saboda yanayi irin na cinkoso da hayaniya, bata gari kamar masu yankan aljihu suna amfani da wannan damar domin yiwa mutane sata a wurin zabe saboda haka kowa ya tabbatar yana bibiyar wayar salularsa da jakar kudi da sauransu.

7. Ga guji musu da mutane

Akwai mutane masu hali daban-daban a wurin zabe kuma baka san yanayin da mutum ke ciki ba, hakan yasa yana da muhimmanci mutum ya guji musu ko jayaya da mutane a layin zabe saboda kiyaye abin da ba so.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel