Zabe: Sakamako daga jihohin Sokoto, Kebbi da Jigawa
A jiya, Asabar, 23 ga watan Fabarairu ne aka gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majlisar tayya ('yan majalisar wakilai da dattijai) a fadin kasar nan.
Tun a jiyan sakamako su ka fara fitowa daga mazabu daban-daban da ke fadin kasar nan. Sai dai har yanzu hukumar zabe ta kasa (INEC) ba ta fara fitar da sakamako a hukumance ba.
Zaben dai ya fi jan hankali ne a matakin kujerar shugaban kasa tsakanin manyn ‘yan takara; shugaba Buhari a jam’iyyar APC da babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP.
Manema labarai da ‘yan jarida sun fi mayar da hankali a kan sakamakon mazabun manyan ‘yan siyasa da ke goyon bayan ‘yan takarar biyu.
A yayin da aka kammala kad'a kuri'u a wasu sassa na jihohi 36 na kasar Nigeria, ciki kuwa har da jihohin Sokoto, Jigawa da Kebbi, tuni aka fara tattara kuri'u tare da kidaya su a wasu rumfunan zabe na jihohin.
DUBA WANNAN: Da duminsa: Buhari ya kayar da Atiku a mazabar Obasanjo
HATTARA: Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ce kadai ke da ikon tattara kuri'u da fadin sakamakon zabe. Bayanai a kan sakamakon kuri'un da aka kad'a a mazabun da zaka karanta a wannan shafin ba daga hukumar INEC ya ke ba. Legit.ng Hausa ba za ta iya tantance gaskiyar sakamakon ba.

Asali: UGC
Rahotannin da muka samu yanzunan yana nuna cewa jam'iyyar APC ne ta lashe zabe a rumfar zabe na gidan gwamnatin jihar Sokoto.
Sokoto, government house PU 008
Zaben shugaban kasa
APC - 190
PDP - 104
Zaben Sanata
APC - 169
PDP - 148
Zaben Majalisar Wakilai
APC - 168
PDP - 148
A halin yanzu dai sakamakon zabe sun fara shigowa daga akwutanan zabe, duba sakamakon a kasa:
Sarkin Yakin Binji, 008 Sokoto South Local government, Jihar Sokoto
Zaben kujerar shugaban kasa
PDP — 72
APC — 63
NUP — 1
PPA — 2
Lalatacen kuri'a — 1
Zaben kujerar Sanata
PDP — 75
APC — 63
APDA — 1
Invalid —
Zaben kujerar wakilai na tarayya
PDP —71
APC — 69
Sarkin Adar Kwanni 008 A, Sokoto South LGA, Sokoto North, Sokoto.
Zaben kujerar shugaban kasa
PDP: 65
APC: 99
Zaben kujerar Sanata
PDP: 63
APC: 97
Zaben kujerar wakilai na tarayya
PDP: 66
APC: 94
Jihar Sokoto
- Jimillar masu kada kuri'a = 1,726,887
- 'Yan takarar shugabannin kasa masu karfi
* Muhammadu Buhari - APC
* Atiku Abubakar - PDP
- Yan takarar Sanatoci masu karfi mazabar Sokoto ta Gabas
* Ibrahim Abdullahi Gobir - APC
* Maidaji Shehu - PDP
- Yan takarar Sanatoci masu karfi mazabar Sokoto ta Arewa
* Aliyu Magatakarda Wamako - APC
* Ahmed Maccido Muhammad - PDP
- Yan takarar Sanatoci masu karfi mazabar Sokoto ta Kudu
* Abubakar Tambuwal Shehu - APC
* Ibrahim Danbaba Abdullahi - PDP
Mata sunyi tururuwar fitowa wurin zabe a Sokoto
Dubban mata ne suka fito domin kada kuri'arsu a rumfunan zabe daban-daban na jihar Sokoto a inda aka fara zaben tun karfe 8.35 na safiyar yau.
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya kada kuri'arsa misalin karfe 11:52 na safiya a mazabarsa ta 001 Kofar Ajiya da ke karamar hukumar Tambuwal.
Jim kadan bayan kada kuri'arsa, Tambuwal ya ce zabe yana tafiya lami lafiya a jihar kuma ya gamsu da yadda ma'aikatan zaben ke aikinsu.
Ya ce jam'iyyarsa za ta amince da dukkan sakamakon da hukumar zabe ta fitar.
Dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Sokoto, Alhaji Ahmad Aliyu yayin da ya ke jefa kuri'arsa a magajin rafi anna ward a jihar Sokoto.
A halin yanzu dai sakamakon zabe sun fara shigowa daga akwutanan zabe, duba sakamakon a kasa:
Sarkin Yakin Binji, 008 Sokoto South Local government, Jihar Sokoto
Zaben kujerar shugaban kasa
PDP — 72
APC — 63
NUP — 1
PPA — 2
Lalatacen kuri'a — 1
Zaben kujerar Sanata
PDP — 75
APC — 63
APDA — 1
Invalid —
Zaben kujerar wakilai na tarayya
PDP —71
APC — 69
Sarkin Adar Kwanni 008 A, Sokoto South LGA, Sokoto North, Sokoto.
Zaben kujerar shugaban kasa
PDP: 65
APC: 99
Zaben kujerar Sanata
PDP: 63
APC: 97
Zaben kujerar wakilai na tarayya
PDP: 66
APC: 94
Jihar Jigawa
Jimillar masu kada kuri'a = 1,702,721
- 'Yan takarar kujerar shugaban kasa masu karfi
* Muhammadu Buhari - APC
* Atiku Abubakar - PDP
- Yan takarar kujerar sanata masu karfi mazabar Jigawa ta Tsakiya
* Sabo Muhammad Nakudu - APC
* Mustapha Sule Lamido - PDP
- Yan takarar Sanatoci masu karfi mazabar Jigawa ta Arewa maso Gabas
* Mohammed Ubali Shittu - PDP
* Ibrahim Hassan - APC
- Yan takarar Sanatoci masu karfi mazabar Jigawa ta Arewa maso Yamma
*Sankara Danladi Abdullahi - APC
* Umar Nasiru Roni - PDP
Jigawa (Hadejia)
Yankoli Ward 05
Presidential
ADPA 1
C4C 1
MMN 2
APC 301
PDP 19
Senate
APC 203
PDP 99
SDP 27
MPN 1
ADC 1
Invalid 10
Representatives
APC 173
PDP 30
SDP 140
AA 1
PT 1
ADC 1
Invalid 9
A tuni dai Gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru ya riga ya kada kuri'ansa a safiyar yau a garin babura inda kuma ya yi kira ga al'umma su fito kwansu da kwarkwata su zabi dan takarar da suka ra'ayi.
A halin yanzu dai an kammala raba kayayakin aiki a karamar hukumar Hadejia na sai dai mutane ba su fito sosai ba.

Asali: Twitter
Rahoton da muka samu daga Daily Trust ya nuna cewa an samu jinkirin fara zabe a kauyen Sundi Mina da ke karamar hukumar Birnin Kudu na jihar Jigawa.
Rahoton ya bayyana cewa har zuwa karfe 10 na safiya jami'an zabe ba su gama karbo kayayakin zabe daga hedkwatan jihar ba kuma masu kada kuri'a suna can suna jira.
Duk da jinkirin da aka samu da farko, zabe ya fara kankama a sassan jihar Jigawa.
Sakamakon zabe na jihar Jigawa sun fara shigowa
Zaben 2019: PU 002, Arewa Primary School, Karamar hukumar Babura , jihar Jigawa
Sakamakon zaben shugaban kasa
APC.. 209
PDP.. 11
SDP... 1
APA... 1
PCP... 1
APDA.. 1
(4 INVALIDS)
Zaben Sanata
PDP... 16
APC.. 171
SDP... 36
(5 INVALID)
P.U 002, Majema, Hadejia LGA, Jigawa Northeast
Zaben shugaban kasa
APC...289
PDP... 30
Senate
APC... 190
PDP.... 88
'Yan majalisar wakilai na tarayya
APC... 177
PDP...61
SDP...36
P.U 007, Makeran Gabas Jigawa North
Zaben shugaban kasa
APC...353
PDP... 20
Senate
APC...220
PDP.... 148
Zaben 'yan majalisun wakilai na tarayya
APC... 194
PDP 0
SDP 11
Jihar Kebbi
- Jimillar masu kada kuri'a = 1,718,180
- 'Yan takarar shugabannin kasa masu karfi
* Muhammadu Buhari - APC
* Atiku Abubakar - PDP
- Yan takarar Sanatoci masu karfi mazabar Kebbi ta Arewa
* Abdullahi Abubakar Yahaya - APC
* Usman Bello Suru - PDP
- Yan takarar Sanatoci masu karfi mazabar Kebbi ta Tsakiya
* Adamu Mainsara Aliero Muhammad - APC
* Shehu Abubakar - PDP
- Yan takarar Sanatoci masu karfi mazabar Kebbi ta Kudu
* Bala Ibn Na Allah - APC
* Benjamin Ezra Dikku - PDP
A halin yanzu rahoton da muka samu daga Daily Trust na cewa Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya gaza kada kuri'arsa saboda matsalar da aka samu wurin tantance katin zabensa.
Sanata Muhammad Adama Aliero ya kada kuri'ansa
Sanata mai wakiltan Kebbi ta Tsakiya kuma dan takarar sanata a zaben 2019, Sanata Muhammad Adamu Aliero ya samu kada kuri'arsa a mazabar sarkin fada 1 da ke jihar Kebbi.

Asali: Original

Asali: Original
Tunatarwa: Domin cigaba da samun labarai a masu dumi-dumi a wannan shafin sai ka/ki rika latsa refreshing a manhajar shiga yanan gizo daga lokaci zuwa lokaci.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng