Jerin garuruwa guda 10 da miyagun yan bindiga suka tasa a mahaifar shugaba Buhari

Jerin garuruwa guda 10 da miyagun yan bindiga suka tasa a mahaifar shugaba Buhari

Ayyukan miyagun mutane yan bindiga na cigaba da ta’azzara tare da fadada a jahar Katsina, musamman ma a yankin karamar hukumar Batsari, Dutsanma, Funtuwa da Dandume, inda yan bindigan suke cin karensu babu babbaka.

Legit.ng ta ruwaito har yanzu yan bindigan sun gagari duk wasu matakai da gwamnati ta dauka tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, inda suke cigaba da kai hare hare a duk inda suka ga dama, kuma a sanda suka ga dama.

KU KARANTA: Ina mazan suke: Yadda wasu Mata suka yi arangama da masu garkuwa da mutane suka samu nasara

Anan ma wasu gungun yan bindigan ne suka halaka wani mutumi a yayin wani samame da suka kai a daren Laraba, 20 ga watan Feburairu inda suka tashi al’ummomin dake zaune a wasu garuruwa guda goma dake cikin karamar hukumar Batsari.

Rahotanni sun bayyana yan bindigan sun kashe wannan mutumi ne a kauyen Ruma Tsohuwa, amma sauran garuruwa goman da suka tasa sun hada da Garin Labo, Garin Yara, Garin Dodo, Shingi, Kasai, Sabon Garin Danburawa, Dantudun da Garin Yara.

Wannan hari ya biyo wani hari na kwana kwanan nan da wasu yan bindigan suka kai a kauyen Kasai cikin karamar hukumar Batsarin kuma dai, inda suka kashe mutane biyar, sa’annan suka kashe jami’in Soja guda daya.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar da cewa fiye da mata da kananan yara dubu biyu ne suka rasa matsuguninsu a sakamakon harin na daren Laraba, inda tace yawancin yan gudun hijiran sun samu mafaka ne a makarantar Firamarin gwamnati dake Batsari.

“Yan bindigan sun cigaba da kai hare hare a kowanne dare, suna kai hari kauyuka biyu a kowanne dare, na karshen da suka kai a daren Laraba shi ne a kauyen Ruma tsohuwa, inda suka kashe mutum guda, suka yi awon gaba da dabbobi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel