Harin kwanton bauna: Dakarun soji sun kashe mayakan Boko Haram 5, ta kwaci makamai (Hotuna)

Harin kwanton bauna: Dakarun soji sun kashe mayakan Boko Haram 5, ta kwaci makamai (Hotuna)

A kalla mayakan kungiyra Boko Haram ne su ka gamu da ajalin su a wani hambararre hari da su ka yi yunkurin kai wa sansanin soji a Buni Yadi a karamar hukmar Gujba da ke jihar Yobe a yammacin jiya, Asabar, 16 ga watan Fabarairu.

Mayakan na kungiyar Boko Haram sun nufi sansanin sojin cikin shirin kai mummunan hari da muggan makamai da su ka hada da motar yaki, manyan bindigu samfurin AK 47 guda 9, bindigar harbor jirgin sama guda 1, bama-bamai guda 4, alburusai ma su yawa da sauran su. Sai dai mayakan sun gaza samun nasara a kan dakarun soji.

A sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce babban soja daya da wasu kananan sojoji 3 sun rasa ran su yayin da wasu biyar su ka jikkata a musayar wuta da mayakan ta kungiyar Boko Haram.

Harin kwanton bauna: Dakarun soji sun kashi mayakan Boko Haram 5, ta kwaci makamai (Hotuna)

Dakarun soji sun kwaci makamai
Source: Twitter

Harin kwanton bauna: Dakarun soji sun kashi mayakan Boko Haram 5, ta kwaci makamai (Hotuna)

Dakarun soji sun kashe mayakan Boko Haram 5
Source: Twitter

Harin kwanton bauna: Dakarun soji sun kashi mayakan Boko Haram 5, ta kwaci makamai (Hotuna)

Makaman mayakan Boko Haram
Source: Twitter

Harin kwanton bauna: Dakarun soji sun kashi mayakan Boko Haram 5, ta kwaci makamai (Hotuna)

Dakarun soji sun kashi mayakan Boko Haram 5, ta kwaci makamai
Source: Twitter

Sojojin sun yi nasarar kwace makamai da dama daga hannun ‘yan ta’addar kungiyar Boko Haram.

A jiya, Asabar, ne Legit.ng ta rawaito cewar mayakan kungiyar Boko Haram sun kai farmaki a sansanin sojoji na 27 task force brigade da ke Buni yadi a jihar Yobe kamar yadda mazauna kauyen suka bayyana.

Legit.ng ta gano cewar 'yan ta'addan sun kai farmaki garin ne misalin karfe 5.30 na yamma inda suka iso cikin motocci masu dauke da bindigu da ragowar wasu muggan makamai.

DUBA WANNAN: Kisan mutane 66 a Kaduna: El-Rufa'i ya ziyarci kauyukan karamar hukumar Kajuru (Hotuna)

Wani shaidar gani da ido da ya nemi a boye sunansa ya ce 'yan ta'adan sun shigo garin ne ta kauyen Amiya da ke kudancin garin sannan suka fado tsakiyar garin.

"Ba su taba kowa ba, sun wuce zuwa sansanin sojojin ne sannan suka fara musayar wuta da sojojin. Mu kuma duk mun tsere domin neman mafaka," inji shi.

Sannan ya kara da cewa mazauna kauyen sun shige daji domin su tsira da ransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel