Madalla: APC ta fara sa rai a Jihar Zamfara bayan an dakatar da zabe

Madalla: APC ta fara sa rai a Jihar Zamfara bayan an dakatar da zabe

Mun ji cewa manyan jam’iyyar APC mai mulki a Zamfara sun yi farin cikin jin labarin cewa an dakatar da zaben da aka shirya a cikin karshen makon nan. Jam’iyyar tana gani hakan zai yi mata amfani.

Madalla: APC ta fara sa rai a Jihar Zamfara bayan an dakatar da zabe

APC na sa ran cewa ayi zabe a jihar Zamfara da ita
Source: Facebook

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridun kasar nan, wasu manyan APC sun nuna farin cikin su game da dage zabe da aka yi zuwa mako mai zuwa. Wasu jagororin jam’iyyar sun bayyana haka a wata hira da aka yi da su jiya.

Alhaji Sha’ayau Sarkin-Fawa wanda yana cikin kusoshin APC a jihar Zamfara, ya bayyanawa manema labarai cewa matakin da aka dauka, zai ba jam’iyyar dama ta shiga zaben gwamnoni da majalisa bayan a da an haramta masu.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC tayi tir da dage zabe da aka yi a Najeriya

Sha’ayau Sarkin-Fawa yake cewa bayan jihar Zamfara, har a Ribas inda kotu ta hana jam’iyyar APC takara, wannan mataki zai yi wa amfani. Alhaji Sarkin-Fawa yace har ga Allah sun ji dadin jin cewa an dakatar da zaben.

Jigon na APC yana sa rai wannan rarar lokaci da aka bada zai bada dama APC ta jefa ‘yan takarar ta a zaben majalisa da kuma gwamnoni a wadannan jihohi. A makon jiya ne Kotu ta nemi INEC ta bar APC ta shiga takaran na 2019.

Shi ma wani babban jagoran APC a jihar ta Zamfara, Alhaji Bello Maliki, ya nuna jin dadin sa bayan an dage wannan zabe. Bello Maliki yace dama can an aikawa hukumar takarda ana neman ta dage zaben ko APC za ta samu shiga.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel