Shekaru ya shirya taron gabatar da addu’o’I na musamman game da zaben gobe

Shekaru ya shirya taron gabatar da addu’o’I na musamman game da zaben gobe

Yau take jajibarin zabe, yayin da a gobe ranar Asabar, 16 ga watan Feburairu za’a gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya, zaben da aka dade ana jiransa, wanda ake sa ran fafatawa tsakanin manyan yan takarar da suka hada da shugaban kasa Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Da wannan ne ake ta yi ma yan Najeriya kiraye kirayen su gudanar da addu’o’i na musamman don ganin an gudanar da zaben cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, a tashi yan kallo lafiya, yan wasa ma lafiya.

KU KARANTA: Bincike ya tabbatar akwai isashshen sinadarin iskar gas a Gombe da Bauchi – shugaban NNPC

Shekaru ya shirya taron gabatar da addu’o’I na musamman game da zaben gobe
Shekaru ya shirya taron gabatar da addu’o’I na musamman game da zaben gobe
Asali: Facebook

Anan tsohon gwamnan jahar Kano Malam Ibrahim Shekarau, kuma tsohon dan takarar shugabancin Najeriya, wanda a yanzu haka yake takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, ne ya shirya addu’o’i na musamman.

Shekarau ya shirya wannan taron addu’a ne a gidansa dake fadar Mundubawa a cikin garin Kano, wanda shi da kansa ya jagoranta, inda aka yi addu’ar samun zaman lafiya a Najeriya a yayin zaben tare da nema ma kansa nasara a takarar da ya fito.

Shekaru ya shirya taron gabatar da addu’o’I na musamman game da zaben gobe
Shekaru ya shirya taron gabatar da addu’o’I na musamman game da zaben gobe
Asali: Facebook

A wani labarin kuma Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ko kadan baya shakkar fuskantar dan takarar Kwankwaso, Sani Aliyu Madakin Gini a takarar da suke yi, inda yace jama’a ne zasu tabbatar da mai nasara a tsakaninsa da dan takarar Kwankwaso, Madakin Gini.

“Dalilin shigata siyasa shine don na bauta ma jama’a ta hanyar sadaukar da kaina, don haka a matsayina na tsohon gwamna daya kwashe shekaru takwas bisa karagar mulki, ina da kyakkyawar fahimtar matsalolin da jama’ana ke fuskanta.

“Saboda haka bana jin tsoro ko shakka indai jama’a ne zasu zabi wanda suke so, ni kam naso ace da Kwankwaso zan fafata, domin kuwa a Kwankwaso Sanata ne dan bakara, bai taba taka kafarsa a Kano ba tun shekaru uku da rabi da suka gabata. Bai taba ganawa da al’ummar mazabarsa a cikin shekarun nan ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel