Bincike: Yawan 'yan Najeriya dake cikin matsanancin Talauci ya kai 91m

Bincike: Yawan 'yan Najeriya dake cikin matsanancin Talauci ya kai 91m

- Sama da yan Najeriya biliyan 91 ne suka rayuwa cikin tsantsar talauci

- Najeriya ta shiga cikin jerin kasashen da al'ummar ta ke fama da talauci a duniya

- A cikin kowanne minti 1 mutane Shida ke fadawa cikin talauci

Bincike: Yawan 'yan Najeriya dake cikin matsanancin Talauci ya kai 91m

Bincike: Yawan 'yan Najeriya dake cikin matsanancin Talauci ya kai 91m
Source: Getty Images

Bisa ga binciken da World Poverty Clock ya gudanar ya bayyana cewa a kalla mutane miliyan 3 ne suka fada cikin talauci a Najeriya daga watan Nuwamba shekara ta 2018 zuwa watan Fabrairu shekara ta 2019.

Bisa ga binciken da World Data Lab ya fitar daga birnin Vienna, ya nuna cewa a kalla 'yan Najeriya miliyan 91 ne suke rayuwa a kasa da dalar amurka Daya a kowacce rana har zuwa 13 ga watan nan da muke ciki.

A watan Yulin shekara ta 2018 ya tabbata cewa Najeriya ta doke kasar India a matsayin kasar da tafi kowa fama da talauci da mutane miliyan 86.9.

Prime minister na British Theresa May ya kara tabbatar da hakan inda yace Najeriya ta shiga cikin jerin kasashen da al'ummar ta ke fama da talauci a fadin duniya.

"Yawan adadin 'yan Najeriya dake fama da talauci yana kara hauhawa wanda a halin yanzu mutane miliyan 87 suna rayuwa a kowacce rana da kasa da dalar amurka Daya inda Najeriya a halin yanzu ta doke kowacce kasa a bangaren talauci" cewar Shugabar Ingila

GA WANNAN: Wannan zaben yafi kowanne razana ni - Prof. Bolaji Akinyemi

Tun lokacin da May tayi wannan jawabi a South Africa a watan Agusta adadin masu fama da talaucin ya kara hauhawa zuwa miliyan 91.16 inda a kowanne minti daya mutane shida ne ke fadawa cikin wannan hali.

Bisa ga zaben shekara ta 2019 shugaban kasa Muhammad Buhari da abokin karawar sa Atiku Abubakar suna amfani da wannan hali na talauci a matsayin wani makamin kamfe a garesu.

Gwamnatin Buhari tana cewa ita gwamnati ce dake kulawa da walwalar talakawa yayin da su kuma magoya bayan Atiku suke cewa an shiga wannan hali ne sanadiyyar wannan gwamnatin meci a yanzu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel