2019: Tsagerun Neja Delta sun yiwa kudirin Atiku mubaya'a

2019: Tsagerun Neja Delta sun yiwa kudirin Atiku mubaya'a

Yayin da ya rage sauran kwanaki biyu kacal a gudanar da babban zaben kujerar shugaban kasa na ranar Asabar ta jibi, kungiyar tsagerun Neja, ta yi karin haske dangane da wanda za ta yiwa mubaya'a a yayin babban zabe na kasa.

A yayin da ya rage sauran kwanaki kalilan a gudanar da babban zaben kujerar shugaban kasa na ranar Asabar, 16, ga watan Fabrairu, kungiyar tsagerun Neja Delta ta Niger Delta Avengers, NDA, ta bayyana mubaya'a ta goyon bayan dan takara na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Cikin wata sanarwa da sa hannun kakakin ta, Mudoch Agbiniho, kungiyar ta yi watsi da dattawan ta yayin da su ka yi yunkuri na goyon baya tare da tabbatar da mubaya'ar su kan kudirin tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari.

2019: Tsagerun Neja Delta sun yiwa kudirin Atiku mubaya'a
2019: Tsagerun Neja Delta sun yiwa kudirin Atiku mubaya'a
Asali: UGC

Kungiyar tsagerun cikin kiran ta na janyo hankali, ta ce al'ummar kasar nan su fara shirye-shiryen fuskantar mugun matsi na tattalin arziki muddin shugaba Buhari ya yi nasara a yayin zaben jibi na Asabar ta hanyar magudi.

NDA ta yi barazana gami da shan alwashi na daura damara tare da zage dantsenta wajen 'dai'daita tattalin arzikin kasar nan muddin Buhari ya yi nasara ta hanyar magudi ko kuma wani nau'i na rashin gaskiya.

KARANTA KUMA: Ya kamata Buhari ya bari a yiwa Amaechi gwaji na ta taɓuwar hankali - Wike

Cikin gargadi da kira na tabbatar da zabe da ya tsarkaka da gaskiya, kungiyar NDA ta ce ba za ta gaza ba wajen fasa bututun mai tare da haramta gudanar man fetur cikin magudanan sa da ke fadin kasar nan kasancewar sa babban arziki da ta dogara da shi.

Kazalika kungiyar cikin sanarwar da ta wassafa ta kuma bayyana amincin ta kan kudirin Atiku na sauya fasalin kasar nan tare da yi ma ta garambawul yayin da akalar jagoranci ta koma karkashin gudanarwar sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel