Cikin Hotuna: Taron yakin zaben Buhari a garin Abuja

Cikin Hotuna: Taron yakin zaben Buhari a garin Abuja

A yau Laraba, 13 ga watan Fabrairu, shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyya mai ci ta APC, ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe cikin babban birnin kasar nan na tarayya Abuja.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya nufaci babban filin taron kasar nan na Eagle Square da ke garin Abuja bayan halartar taron rattaba hannu kan yarjejeniyar aminci da tabbatar da zaman lafiya gabani da kuma bayan babban zabe.

Yayin isowar shugaba Buhari filin taro na Eagle Square

Yayin isowar shugaba Buhari filin taro na Eagle Square
Source: Twitter

Yayin isowar shugaba Buhari filin taro na Eagle Square

Yayin isowar shugaba Buhari filin taro na Eagle Square
Source: Twitter

Taron yakin zaben Buhari a garin Abuja

Taron yakin zaben Buhari a garin Abuja
Source: Twitter

Tururruwar al'umma yayin taron yakin zaben Buhari a garin Abuja

Tururruwar al'umma yayin taron yakin zaben Buhari a garin Abuja
Source: Twitter

Tururruwar al'umma yayin taron yakin zaben Buhari a garin Abuja

Tururruwar al'umma yayin taron yakin zaben Buhari a garin Abuja
Source: Twitter

Taron yakin zaben Buhari a garin Abuja

Taron yakin zaben Buhari a garin Abuja
Source: Twitter

A yayin da a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, za a gudanar da babban zabe na kasar nan, a yau kuma shugaba Buhari da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar amincewa da duk yadda sakamakon zaben zai kasance.

Baya ga amincewa da sakamakon zabe, kazalika yarjejeniyar ta hadar ta shan alwashi na tabbatar da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali gami da lumana gabani da kuma bayan zabe tsakanin manyan 'yan takarar biyu.

KARANTA KUMA: Rayukan Mutane 14 sun salwanta yayin yakin zaben Buhari a jihar Ribas

Cikin wani rahoto mai nasaba da wannan, a yau ne jam'iyyar PDP ta shirya gudanar da taron ta na yakin zaben kujerar shugaban kasa cikin garin Abuja, inda daga bisani ta janye tare da daukar dangana sakamakon yadda jam'iyya mai ci ta APC ta yi ma ta kaka-gida.

Bidiyo yayin isowar shugaba Buhari filin taro na Eagle Square

Ku biyo mu kadan...

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel