Lamidon Adamawa, da wasu manyan Sarakunan Najeriya 2 dake tare da Buhari a zaben 2019

Lamidon Adamawa, da wasu manyan Sarakunan Najeriya 2 dake tare da Buhari a zaben 2019

A yau saura kwanaki biyar cur a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, wanda ake sa ran da ikon Allah zai gudana a ranar 16 ga watan Feburairu na shekarar 2019 a dukkanin jihohi 36, kananan hukumomi 774 na Najeriya.

Sai dai yayin da zaben ke karatowa, yan siyasa da yan takara suna cigaba da neman goyon bayan al’ummominsu, daga ciki har da talakawa, matasa, mata, Malamai, attajirai, yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati, Sarakuna da sauransu.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan majalisa a jahar Sakkwato

Lamidon Adamawa, da wasu manyan Sarakunan Najeriya 2 dake tare da Buhari a zaben 2019

Lamidon Adamawa, da Buhari
Source: Facebook

Idan za’a tuna, kimanin makonni biyu da suka gabata ne wasu manyan kungiyoyin kabilun Najeriya da suka hada da kungiyar dattawan Arewa, hadaddiyar kungiyar yarbawa, hadaddiyar kungiyar Inyamurai da kuma kungiyar dattawan Neja Delta suka bayyana goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar.

Don haka anan ma Legit.ng ta kawo muku jerin wasu manyan Sarakunan Najeriya masu daraja ta daya da suka bayyana tare da furta goyon bayansu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fili, ba tare da boye boye ba.

Lamidon Adamawa, da wasu manyan Sarakunan Najeriya 2 dake tare da Buhari a zaben 2019

Sarkin Legas
Source: Facebook

Duk da cewa dai an san Sarakuna da nuna kawaici da kuma kokarin nuna suna tare da bangare, amma wadannan manyan Sarakuna guda uku sun bayyana ma Duniya suna tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarinsa na zarcewa karo na biyu.

Daga cikinsu akwai;

Lamidon Adamawa Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa

Sarkin Legas Oba Rilwan Akiolu

Sarkin Aba Dakta Isaac A. Ikonne

Lamidon Adamawa, da wasu manyan Sarakunan Najeriya 2 dake tare da Buhari a zaben 2019

Sarkin Aba
Source: Facebook

Mai martaba Lamidon Adamawa ya bayyana goyon bayansa ga Buhari ne a ranar 7 ga watan Feburairu, yayin da Buhari ya kai masa gaisuwan ban girma a fadarsa dake garin Yola, shi kuwa Sarkin Legas (Oba of Lagos) ya yi mubaya’a ga Buhari ne a ranar Asabar 9 ga watan Feburairu, sai kuma Sarkin Aba (Enyi 1 of Aba) daya furta goyon bayansa ga Buhari a ranar 29 ga watan Janairu a jahar Abia.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel