Jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya da ba su taba sauya sheka ba

Jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya da ba su taba sauya sheka ba

Canja jam'iyyar siyasa ko kuma sauya sheka abu ne wadda ke faruwa a duk inda ake mulkin demokradiya musamman a lokutan da zabuka suka matso. 'Yan siyasa na canja jam'iyya ne saboda dalilai masu yawa da suka hada da rashin jituwa, rashin kulawa, rashin samun tikitin takara, kora da makamantansu.

Sai dai duk da hakan akwai wasu 'yan siyasar da ba su taba ficewa daga jam'iyyun siyasar su ba tunda suka shiga siyasar. A yau zamu kawo muku wasu daga cikin fitattun 'yan siyasar Najeriya ne da ba su taba sauya sheka ba tun daga 1999 da Najeriya ta mayar da mulki ga farar hula zuwa yanzu.

Ga wasu daga cikin fitattun 'yan siyasan:

Ahmed Makarfi: Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya shiga jam'iyyar PDP ne a 1998. Bayan ya sauka daga gwamna ya zama Sanata a shekarar 2007 sannan daga bisani ya zama shugaban PDP na rikon kwarya har zuwa lokacin da jam'iyyar ta zabi sabon shugaba. Duk gwagwarmayar da akayi a PDP, Makarfi bai taba ficewa daga jam'iyyar ba.

Sule Lamido: Yana daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar PDP a 1998 kuma ya yi ministan harkokin waje daga 1999 zuwa 2003 a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Ya kuma yi gwamna sau biyu a jiharsa ta Jigawa kuma a halin yanzu shine jagoran jam'iyyar PDP a jiharsa kuma bai taba sauya sheka zuwa wata jam'iyya ba.

Bola Ahmed Tinubu: Tinubu dan siyasa ne da ya yi fice ba a jiharsa ta Legas kadai ba har ma a kasa baki daya. Yana daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar AD a 1998 amma daga baya jam'iyyar ta hade da wasu jam'iyyun siyasa biyu suka kafa APC. Tun daga lokacin Tinubu bai taba ficewa daga jam'iyyar ba.

Goodluck Jonathan: Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shima bai taba fita daga jam'iyyar PDP ba tun lokacin da ya ke mataimakin gwamna a jiharsa ta Bayelsa har ya zama mataimakin shugaban kasa daga bisani ya zama shugaban kasa. Yana daga cikin iyayen jam'iyyar PDP na kasa.

Ahmed Sani Yariman Bakuri: Tsohon gwamnan jihar Zamfara shima ya shiga ANPP ne a 1998 inda ya zama gwamna daga 1999 zuwa 2007. Yarima ya kuma zama Sanata a 2007 har yanzu inda ya ke wakiltan mazabar Zamfara ta Yamma.

Abdul Ahmed Ningi: Abdul Ningi jigo ne a jam'iyyar PDP reshen jihar Bauchi. Yana daga cikin wadanda suka shiga PDP tun a 1998 kuma ya zaman dan majalisar wakilai a 1999 zuwa 2011 sannan ya zama Sanata tsakanin 2011 zuwa 2015.

Kashim Shettima: Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno shima bai taba sauya sheka ba tun lokacin da ya fara siyasa. Asali ya fara daga jam'iyyar ANPP ne kuma ya cigaba da kasancewa a APC bayan ANPP tayi gammaya da wasu jam'iyyu inda aka kafa APC.

Sauran 'yan siyasan da ba su taba sauya sheka ba sun hada da: Ibrahim Shehu Shema na APC, Abdulkadir Balarabe Musa na PRP, Usman Bugaje na APC, Emeka Ihedioha na PDP, Ibrahim Geidam na APC, Muntari Shehu Shagari na PDP da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel