Hayaniya, fushi da cece-kuce bayan da aka yiwa soji 200 ritaya

Hayaniya, fushi da cece-kuce bayan da aka yiwa soji 200 ritaya

- Hayaniya ta tashi a hukumar sojin Najeriya saboda ritayar ba zata

- A ranar 8 ga watan Fabrairu ne aka damka wa sojojin da suka halarci makarantar sakandaren soja takardar ritaya

- Wasu daga cikin sojojin basu kai shekaru 35 suna aiki ba kuma basu kai shekaru 60 a duniya ba

Hayaniya, fushi da cece-kuce bayan da aka yiwa soji 200 ritaya
Hayaniya, fushi da cece-kuce bayan da aka yiwa soji 200 ritaya
Asali: UGC

Majiya mai karfi daga hukumar sojin Najeriya ta sanar damu yanda hatsaniya ta fara lokacin da shugaban sojin kasa, Lt General Tukur Buratai, ya umarci sakataren sojin da ya bada sanarwar ritaya ga sojojin da sukayi karatun sakandare a NMS Zaria, inda sukayi shekaru biyar.

Umarnin shugaban sojin shine shekaru biyar da sukayi a makarantar sojojin a kara ta akan shekarun aikin su.

Mai magana da yawun sojin, Janar Sani Usman, wanda yakamata ace ya maida martani akan wannan cigaban, yana daya daga cikin sojojin da abun ya shafa.

Amma kuma, wata majiyar mu wacce take makusanciya ga hukumar sojin tayi bayani a ranar asabar cewa hukuncin ya shafi "kusan sojoji 200" kuma hakan ya biyo bayan "sabuwar dokar gwamnatin tarayya ne."

Majiyar ta kara da cewa dokokin anyi su ne don ana bukatar sauran aiyukan subi dokar amma har yanzu basu fara ba.

Majiyar ta kara da cewa duk wadanda abin ya shafa sun karbi takardar sallamar su a 8 ga watan Fabrairu kuma anyi bayanin cewa zasu aje aiki ne a ranar sai dai wasu zasu kai 8 ga watan Maris don su kammala shirye shirye sannan su bar aikin.

Kamar yanda majiyar ta fada, gwamnati tace lokacin da sojojin ke makarantar ana biyansu albashi saboda haka ne shekarun suka shiga cikin na aikin su.

GA WANNAN: Kyan yaba alheri, riqe amana: Masu fanshon Nigeria Airways sun shirya wa zaben makon gobe tsaf

Amma kuma an gano cewa da yawan sojojin da abin ya shafa basu halarci jami'ar sojojin ba daga kammala sakandaren sojojin don samun shaidar digiri kafin shiga aikin sojan.

Da yawan tsofaffin yan makarantar sakandaren sojojin wadanda a halin yanzu sojoji ne an musu ritaya ne ta dole cikin kwanaki 3 zuwa 4.

Wata majiyar mai ban haushi ta tabbatar da an tirsasa sojojin ritaya ne bayan basu yi shekaru 35 suna aiki ba ko kuma sun kai shekaru 60 ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel