'Kiyasi: Sakamakon zaben 2019 cikin wasu jihohin Najeriya tsakanin Buhari da Atiku

'Kiyasi: Sakamakon zaben 2019 cikin wasu jihohin Najeriya tsakanin Buhari da Atiku

A sakamakon nazarin wani bincike da manema labarai na jaridar The Nation suka gudanar ya bayyana yadda al'ummar wasu jihohin kasar nan za su jefa kuri'un su yayin babban zaben kujerar shugaban kasa da ke ci gaba da karatowa.

Kamar yadda masu sharhi akan harkokin siyasa suka zayyana, kabilanci a yayin babban zabe ba zai yi tasiri ba wajen rinjayar da nasarar takarar kujerar shugaban kasa tsakanin Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da kuma dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

'Kiyasi: Sakamakon zaben 2019 cikin wasu jihohin Najeriya tsakanin Buhari da Atiku

'Kiyasi: Sakamakon zaben 2019 cikin wasu jihohin Najeriya tsakanin Buhari da Atiku
Source: UGC

Cikin azancin magana masu sharhin sun bayyana cewa, kasancewar mahaifa daya ta Arewa da 'yan takarar biyu ke tarayya da juna, ya sanya yankin Gabas da Yammacin Najeriya zai yi tasiri wajen tantance sakamakon babban zabe na bana.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin da za a gudanar da zaben kujerar shugaban kasa a ranar 16 ga watan Fabrairu na shekarar da muke ciki, Atiku da Buhari na ci gaba da shawagi da karade jihohi 36 da ke fadin kasar nan domin neman magoya baya.

KARANTA KUMA: Kamfe: Atiku ya gudanar da taron yakin zaben sa a jihar Borno da Yobe

A yayin da manyan 'yan takarar biyu ke ci gaba da gudanar da yakin su na zabe cikin salo mabambanta, masana ilimin siyasar yayin ci gaba da hasashe gami da kiyasi akan sakamakon zaben sun bayyana yadda Atiku da Buhari za su kaya cikin wasu jihohin kasar nan.

Ga yadda kiyasi ya kama kamar yadda suka wassafa yayin rinjayar da nasarar jam'iyyar APC ko PDP cikin jihohin Najeriya da ke yankin Kudu maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya:

Kudu maso Yamma

Legas - APC

Oyo - APC

Ogun - APC

Ondo - APC

Ekiti - APC

Osun - APC

Arewa ta Tsakiya:

Benuwe - PDP

Kwara - APC/PDP

Filato - APC/PDP

Nasarawa - APC

Neja - APC

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel