Tare da duba cancanta, ku zabi 'yan takara daidai da ra'ayin ku - Buhari

Tare da duba cancanta, ku zabi 'yan takara daidai da ra'ayin ku - Buhari

A yayin da 'yan kwanaki kalilan suka rage a gudanar da zaben shugaban kasa, a yau Talata cikin jihar Imo, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci al'ummar Najeriya dangane da 'yan takara da suka cancanci a kada ma su kuri'u a zaben bana.

A yau Talata yayin taron sa na yakin neman zabe, baya ga ra'ayi da kuma akida, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi al'ummar jihar Imo kan zaben 'yan takara da suka cancanta ta fuskar riko da akalar jagoranci.

Buhari yayin yakin neman zaben sa a jihar Imo

Buhari yayin yakin neman zaben sa a jihar Imo
Source: Facebook

Shugaban kasar ya bayyana cewa, baya ga duba cancanta, al'ummar Najeriya su tabbatar da zaben 'yan takara masu kishin kasa ba tare da duba ya zuwa akidar su ta addini ko kuma jam'iyya ta siyasa.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaban kasa Buhari ya ce, a halin yanzu zaben 'yan takara masu akida ta tabbatar da hadin kan al'umma da kuma ci gaban kasa itace mafi a'ala wajen fidda kasar nan zuwa Tudun tsira.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yau cikin birnin Owerri yayin taron sa na yakin neman zabe wanda jiga-jigan jam'iyyar sa ta APC suka halarta da suka hadar da shugaban jam'iyyar na kasa, Kwamared Adams Oshiiomhole, Ministan kwadago, Sanata Chris Ngige da kuma Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

KARANTA KUMA: 2019: Ina goyon bayan kudirin tazarcen Gwamna Ganduje - Mahaifin Kwankwaso

Sauran jiga-jigan jam'iyyar da suka take wa Buhari baya sun hadar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, da kuma dan takarar kujerar gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Sanata Hope Uzodinma.

Shugaban kasar da ya jaddada tsayuwar dakan sa ta ci gaba da yaki da rashawa a fadin kasar nan, ya ce gwamnatin sa ta yi kwazon gaske wajen bunkasa harkokin noma, habaka tattalin arziki da kuma yaki da ta'addanci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel