Akwai matsala babba a gidan shari’a a Najeriya – Ag. CJN Tanko Mohammed

Akwai matsala babba a gidan shari’a a Najeriya – Ag. CJN Tanko Mohammed

Sabon CJN watau babban Alkalin Najeriya, Ibrahim Tanko Muhammad, yayi maganar farko bayan hawan sa kujerar Alkalin Alkalai. CJN ya fara magana ne da kokawa da halin da bangaren shari’a ke ciki a Najeriya.

Akwai matsala babba a gidan shari’a a Najeriya – Ag. CJN Tanko Mohammed
CJN ya kaddamar da masu lura da shari’a zabe a babban birnin tarayya Abuja
Asali: UGC

Babban Alkali Muhammad ya bayyana cewa shari’a na cikin wani mawuyacin hali yanzu haka a Najeriya. Sabon Alkalin alkalan kasar yayi kira ga masu ruwa da tsaki da duk wata ta-cewa a harkar shari’a su tashi su ceci kasar.

Alkali Muhammad ya bayyana wannan ne a lokacin da ya kaddamar da wadanda za su lura da korafe-korafen zabe a birnin tarayya Abuja. Sai dai kusan duk manyan Alkalan kotun kolin kasar ba su halarci wannan taro da aka yi ba.

Alkali mai shari’a Tanko Muhammad ya kara nanata cewa Alkalai da masu shari’a su na cikin wani hali a Najeriya, inda yayi kira ga manyan Alkalan sun tashi tsaye wajen ganin an dawowa kotu da kimar da aka san su da ita a Najeriya.

KU KARANTA: Amurka, Birtaniya da EU sun yi tsokaci kan dakatar da Onnoghen

Sabon Alkali Alkalan na rikon kwarya ya fadawa sababbin masu kula da shari’ar zabe su san cewa akwai nauyi da ya rataya a gaban su na yin gaskiya a gaban kuliya. Alkalin ya kuma taya wadanda aka daurawa wannan matsayi murna.

Kamar yadda mu ka samu labari, an fara wannan taro ne da rana da kimanin karfe 3. Manyan Alkalan da su ka halarci taron sun hada da shugabar kotun daukaka kara Zainab Bulkachuwa da kuma babban kotun NIC na kasa Babatunde Adjumo.

A Ranar Juma’a da yamma ne shugaba Muhammadu Buhari ya nada Alkali mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin sabon Alkalin Alkalai na Najeriya bayan dakatar da Mai shari'a Walter Onnoghen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel