Yanzu-yanzu: An nada Bashir a matsayin shugaban riko na NPC

Yanzu-yanzu: An nada Bashir a matsayin shugaban riko na NPC

Gwamnatin tarayya ta amince da nadin Alhaji Hassan Bashir a matsayin shugaban riko na Hukumar Kidayar Jama'a ta Kasa wato National Population Commission.

Sanarwar da ta fito daga Direkta Janar na Hukumar, Dr Ghaji Ismaila Bello a ranar Juma'a a Abuja ta nuna cewa an sanar da nadinsa ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannun Sakataren gwamnatin tarayya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: An nada Bashir a matsayin shugaban riko na NPC
Yanzu-yanzu: An nada Bashir a matsayin shugaban riko na NPC
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kiristoci ne suka taimake ni lokacin da musulmi suka juya min baya - Buhari

Nadin na sa yana zuwa ne bayan karewar wa'addin tsohon shugaban hukumar, Eze Duruiheoma a ranar 23 ga watan Janairun 2019.

Bashir zai rika kula da ayyukan hukumar har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaba. A halin yanzu dai shine ma'aikaci mafi girma a hukumar.

"Kafin nadinsa, Alhaji Hassan Bashir shi ne Kwamishina da ke wakiltan Jihar Bauchi a hukumar ta Kidayar," inji sanarwar

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164