Nasara daga Allah: Sojojin Najeriya sun yi ma mayakan Boko Haram dirar mikiya
Dakarun rundunar Sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara yayin da suka yi dirar mikiya a wani sansanin mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram dake kauyen Makinta Metele cikin karamar hukumar Konduga ta jahar Borno.
Legit.ng ta ruwaito dakarun sun fito ne daga runduna ta 7 na Operation Lafiya Dole, kuma sun samu masaniya game da sansanin Boko Haram din ne ta hanyar wasu bayanan sirri, wanda hakan yasa suka fita farautansu a ranar Alhamis, 24 ga watan Janairu.
KU KARANTA: 2019: Yan takaran Jam’iyyar APC sun yi barazanar tayar da hankali a zaben jahar Ribas

Asali: Facebook
Mataimakin daraktan watsa labaru na rundunar ta 7, Kanal Ado Isa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a da safiyar Juma’a, 25 ga watan Janairu, inda yace Sojoji sun kashe yan Boko Haram guda hudu a yayin samamen.
Haka zalika yace Sojojin sun kwato makamai da suka hada da bindigu guda hudu kirar AK-47, da kuma alburusai da dama, sai kuma kekuna guda uku da yan ta’addan ke amfani dasu wajen zirga zirga a cikin dajin.
Babban kwamandan rundunar ta 7, Birgediya Abdulmalik Bulama Biu ya jinjina ma Sojojin bisa jarumtar da suka nuna wajen samun wannan gagarumar nasara, sa’annan ya mika musu sakon babban hafsan Sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai na godiya da kuma kasancewarsu abin alfahari a gareshi.

Asali: UGC
Haka zalika Buratai ya yi kira a garesu da kasa su yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da sun kawar da mayakan Boko Haram gaba daya daga doron kasa ta yadda zaman lafiya mai inganci zai samu a yankin Arewa maso gabas.
Daga karshe kanal Ado ya nemi jama’a dasu taimaka ma rundunar Sojin Najeriya da ma sauran hukumomin tsaro da bayanan sirri game da ayyukan yan ta’adda a garuruwansu, ta haka ne kadai Sojoji zasu iya magance matsalar, inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng