Kotu ta kwace takarar shugaban kasa daga hannun Jerry Gana
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta soke hukuncin da babban kotun Abuja tayi na mika wa Farfesa Jerry Gana takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben 2019.
A wani zama da kotun tayi a ranar Alhamis karkashin jagorancin Justice Abdul Aboki, ta mayar da takarar jam'iyyar ga tsohon gwamnan jihar Cross Rover, Donald Duke.

Asali: Depositphotos
DUBA WANNAN: Jigo a jam'iyyar APC ya fadi su waye ke tsoron tazarcen Buhari
An sanar da nasarar Duke a matsayin dan takarar shugaban kasar jam'iyyar bayan ya lashe kuri'u 816 a zaben fidda gwani da jam'iyyar tayi a ranar 6 ga watan Oktoban 2018 a yayin da Jerry gana ya samu kuri'u 611.
Sai dai Gana ya garzaya kotu inda ya shigar da kara a dalilin cewa kundin tsarin mulkin jam'iyyar bai bayar da dama Shugaban jam'iyyar da dan takarar shugaban kasa su fito daga yanki guda daya ba.
A kan wannan dalilin ne babban kotun na Abuja ta kwace takarar daga hannun Duke ta mikawa Gana amma kuma yanzu lamarin ya sake canjawa.
Ku biyo mu domin karin bayani ...
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng