Goyon bayan Buhari ya yi sanadiyar mutuwar aure

Goyon bayan Buhari ya yi sanadiyar mutuwar aure

Soyayyar Shugaba Muhammadu Buhari ya yi sanadiyar rabuwar wasu ma'aurata da ke zaune a jihar Filato da ke shiyar Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Abdullahi Yaudau ya yiwa matarsa Hafsat saki biyu ne bayan da ta lashi takobin cewa ita Shugaba Muhammadu Buhari za ta jefawa kuri'a a zaben 2019 kamar yadda Bbc ta ruwaito.

A cewarsa, sun dangana da zuwa wurin iyayenta domin a shawo kan lamarin amma da abin ya gaggara sai ya yanke hukuncin sakinta tare da dukanta har ta balla mata hakori.

Goyon bayan Buhari ya yi sanadiyar mutuwar aure
Goyon bayan Buhari ya yi sanadiyar mutuwar aure
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kiristoci ne suka taimake ni lokacin da musulmi suka juya min baya - Buhari

Majiyar Legit.ng ta yi kokarin tuntubar Hafsat amma hakan bai yiwu ba.

Sai dai an samu ji ta bakin yayanta mai suna Ibrahim Suleima, wanda ya bayyana rashin jin dadinsa a kan yadda lamarin ya kasance.

Ba dai sabon abu bane 'yan uwa ko ma'aurata su kasance suna da banbancin ra'ayi game da siyasa sai dai galibi adawar ba ta cika kai ga irin wannan mataki ba.

A wani rahoton, Legit.ng ta ruwaito muku cewa shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da cewa hukumar ta gama shiri tsaf domin gudanar da zaben na 2019.

Farfesa Mahmood ya tabbatar wa al'umma cewa hukumar za ta gudanar da ingantancen zabe ne akasin yadda wasu jam'iyyun adawa ke ganin kamar hukumar za ta fifita jam'iyyar APC mai mulki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel