Wasu Yaya da Kanwa sun nemi su shiga gidan kurkuku da miyagun kwayoyi

Wasu Yaya da Kanwa sun nemi su shiga gidan kurkuku da miyagun kwayoyi

Mun ji labari dazu nan cewa Jami’an da ke gadin babban kurkukun nan na Kuje sun yi ram da wasu Mata da su kayi kokarin cikin gidan yarin da miyagun kwayoyi. Yanzu dai an cafke wadannan ‘yan mata.

Wasu Yaya da Kanwa sun nemi su shiga gidan kurkuku da miyagun kwayoyi
An yi caraf da wata da ta nemi ta kai kwaya cikin kurkuku
Asali: UGC

Jaridar Punch tace wadannan mata da ‘yan uwan juna ne, sun fada hannun gandurobobin gidan yarin ne a sa’ilin da wata ta nemi kutsawa cikin gidan yarin dauke da tabar wiwi da kuma kwayoyi irin su tramadol mai bugarwa.

Wadannan Bayin Allah da aka kama su na hannun hukuma yanzu haka a babban birnin tarayya. Ainihin wanda aka kama, Miss Blessing Chinwuba ta shiga hannun wani ganduroba ne yayin da ta ke kokarin mika wani kwayoyin.

Kamar yadda mu ka samu labari, an daure miyagun kwayoyin ne a cikin wani kwalin taliya inda aka nemi a mikawa wani da ke tsare a cikin gidan kurkukun mai suna John Ifeanyichukwu. Sai dai a nan take ne, dubun su ta cika.

KU KARANTA: Magajin Malam Aminu Kano ya rasu yana da shekarau 83

Mai magana a madadin sauran gandurobobin babban birnin tarayya Abuja, Humphrey Chukwuedo, shi ne ya sanar da wannan aika-aika da aka shirya a Ranar Litinin dinnan, inda aka dace wani jami’in cikin gidan yarin ya ankara.

Wanda aka kama tace ‘yar uwar tace dai ta mika mawa wannan kwali ba tare da sanin abin da ke ciki ba. Sunana ‘yar uwar da ake zargi Victoria, wanda su ka fito daga gida daya. Ita ma dai Victoria tace sako ne kurum wani ya mika mata.

Kawo yanzu dai Victoria da Yayar ta mai suna Blessing Chinwuba su na hannun hukumar da ke kula da masu harkar miyagun kwayoyi watau NDLEA inda za a tuhume su inji Humphrey Chukwuedo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel