Akwai maha'intan da ke shirin murdiya a zaben 2019 - TY Danjuma
- Tsohon Ministan tsaro, TY Danjuma ya ce a tashi farga kan duk wani yunkuri na tafka magudi yayin zaben gwamnan jihar Taraba a bana
- Danjuma ya yi kira ga al'umma da su tabbatar da kare martabar kawunan su ta hanyar zama lafiya da kwanciyar hankali
- Gwamna Ishaku na jihar Taraba ya nemi al'ummar sa da su tabbatar da yiwa doka da'a gabani da kuma bayan zabe
Tsohon ministan tsaro, Laftanar Janar Theophilus Danjuma mai ritaya, ya ce a tashi a farga kan barazana ta kitimurmurar wasu maha'inta da ke kulle-kullen gindaya wasu munanan ababe na ta'ada domin tafka magudi a zaben 2019.
Tsohon sojan ya yi zargi da cewa a akwai yunkurin gindaya wasu ababe na ta'ada masu tayar da zaune domin cimma nasara ta murdiya ko tafka magudi yayin zaben kujerar gwamnan jihar sa ta Taraba.

Asali: Getty Images
Danjuma wanda ya janyo hankalin al'umma da kuma gwamnatin jihar yayin kaddamar da wasu sabbin dakunan karatu da kuma bincike akan nazarin kimiyya cikin karamar hukumar Takum a jiya Talata, ya gargadi ma su zabe da su dauki akidar nan ta a tsaya a raka kuma a jira a tabbatar.
Yayin ci gaba da gargadin masu kada kuri'u a jihar sa, ya nemi da su kauracewa dukkanin wasu munanan ababe na ta'ada masu tasiri wajen tayar da tarzoma gabanin zabe da kuma bayan sa kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.
Danjuma ya yi kira ga al'ummar jihar da su zauna lafiya tare da tabbatar da kare martabar su gami da 'yanci wajen kada kuri'un su ga gwamnan jihar, Darius Ishaku, domin ci gaba da fantamawa ta sharbar romon dimokuradiyya.
KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Kungiyar Magoya bayan akidar shi'a ta gudanar da zanga-zanga a garin Abuja
Tsohon Ministan yayin fadakarwa ya kuma yi hani ga al'umma da su yiwa kawunan su karatun ta nutsu wajen tsare 'yancin su ta hanyar haramcin sayar da kuri'u ga maha'intan 'yan takara da yunwar mulki ta zame ma su karfen kafa.
A nasa bangaren, Gwamna Ishaku ya yi kira ga dukkanin magoya bayan sa da su tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin su ta hanyar yiwa doka da'a gami da kasancewar su 'yan kasa na gari.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng