Ban fada ba, Atiku ya nesanta kan sa daga wani kalami a kan fadar shugaban kasa

Ban fada ba, Atiku ya nesanta kan sa daga wani kalami a kan fadar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya nesanta kan sa daga wani kalami da aka alakanta da shi na lissafa jami'an shugaba Buhari 30 da ke da laifin cin hanci.

Phrank Shaibu, mai taimakawa Atiku a bangaren yada labarai, ne ya fitar da jawabin amadadin Atiku.

Sai dai babban darektan yakin zaben Atiku kuma tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel, ya ce jawabin bai samu sahalewar Atiku ba.

"Atiku dattijo ne da ba zai ke furta maganar da bashi da hujja a kan ta ba. Mutum ne mai son bin doka da ya ke girmama kundin tsarin mulkin Najeria, a saboda haka ba zai taba yin furucin da ba zai iya kare kan sa a gaban kotu ba," a cewar Daniel.

Da yake magana da manema Labarai a Abuja, Daniel, ya ce 'yan jarida sun yi kuskuren alakanta ra'ayin Shuaibu da furucin Atiku.

Ban fada ba, Atiku ya nesanta kan sa daga wani kalami a kan fadar shugaban kasa
Atiku
Asali: Facebook

A jiya, Litinin, ne kafafen watsa labarai su ka rawaito cewar Shuaibu ya lissafo jiga-jigai a jam'iyyar APC kamar tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran APC na kasa, Bola Tinubu; Shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari, Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan Nasarawa, Abdullahi Adamu; Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal; Shugaban hukumar NTDC, Folarin Coker; Ministan Sadarwa, Lai Mohammed, a matsayin balagurbin mutane da ke tare da Buhari.

DUBA WANNAN: Obasanjo da gumin mahaifina ya ke ci amma ko tunawa da shi ba ya yi - Jami'u

Cikin jerin sunayen akwai hafsin sojin Najeriya, Laftanat Tukur Buratai; Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika; Mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari; Shugaban hukumar tace fina-finai na kasa, Adedayo Thomas; Tsohon gwamnan Bauchi, Adamu Mu'azu; Tsohon gwamnan jihar Osun, Iyiola Omisore; Tsohon shugaban hukumar Fanso na kasa, Abdulrashin Maina; Tsohon karamin Ministan Tsaro, Musliu Obanikoro da Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu.

Sauran sun hada da Gwaman Bauchi, Isah Yuguda; Sanata Godswill Akpabio; Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbanjo; Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje; Tsohon gwamna jihar Jigawa, Saminu Turaki, Sakataren BCDA kuma surukin Buhari, Junaid Abdullahi; tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Wamako; Dan takarar gwamnan APC na jihar Imo, Hope Uzodinma, Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi da gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng