Kamfen: Taron yakin neman zaben Buhari a Damaturu ya bayar da mamaki, hotuna

Kamfen: Taron yakin neman zaben Buhari a Damaturu ya bayar da mamaki, hotuna

- Jirgin yakin neman sake zaben shugaba Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya a karo na biyu ya dira jihar Yobe

- Dubban jama'a sun yi dafifi a garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe, domin ganin shugaba Buhari

- Kafin ya isa jihar Buhari, tawagar yakin neman zaben Buhari ta ziyarci jihar Borno

Jirgin yakin neman zaben shugaba Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya a karo na biyu, karkashin jam'iyyar APC, ya ziyarci jihar Yobe.

Dubun dubatar jama'a ne su ka yi dafifi domin tarba da nuna soyayya da goyon baya ga shugaba Buhari.

Kafin shugaban da tawagar sa su ziyarci garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe, sun fara dira garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, in da su ka kaddamar da yakin neman zaben jam'iyyar APC.

Kamfen: Taron yakin neman zaben Buhari a Damaturu ya bayar da mamaki, hotuna
Taron yakin neman zaben Buhari a Damaturu ya bayar da mamaki
Asali: Twitter

A kalla mutane 12 ne rahotanni su ka bayyana cewar sun raunuka daban-daban a wurin taron kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na Buhari a Maiduguri.

DUBA WANNAN: Zabe: Amurka ta bankado wata makarkashiya da kungiyar Boko Harm da ISIS ke kulla wa

Mutanen sun samu raunukan ne sakamakon turereniyar son ganin shugaba Buhari, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, yayin da ya mike ya karbi lasifika domin gabatar da jawabi a Ramat Square, filin taron kamfen din APC a Maiduguri.

Wata rumfa ce ta karye tare da yin sanadiyar raunta jama'a da dama. Kungiyar bayar da agajin gaggawa ta Red Cross ta garzaya da mutanen da amu raunuka zuwa asibitin kwararru na Maiduguri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel