Atiku ya lissafa sunayen gurbatattun mutane 30 a cikin gwamnatin Buhari

Atiku ya lissafa sunayen gurbatattun mutane 30 a cikin gwamnatin Buhari

Atiku Abubakar, dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP ya lissafa 'gurbatattun' mutane 30 da ke aiki tare da shugaba Muhammadu Buhari.

Mai taimakawa na musamman a fanin watsa labarai, Phrank Shu'aibu ne ya fitar da jerin sunayen a jiya Lahadi kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Ya lura cewa wasu daga cikinsu 'yan jam'iyyar APC ne yayin da sauran kuma sun shiga jam'iyyar ne domin su tsira daga binciken aikata rashawa.

Atiku ya lissafa gurbatattun mutane 30 a cikin gwamnatin Buhari
Atiku ya lissafa gurbatattun mutane 30 a cikin gwamnatin Buhari
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Buhari ya fadi dalilan da yasa har yanzu ake da almajirai a Najeriya

Ya lissafo jiga-jigai a jam'iyyar APC kamar tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran APC na kasa, Bola Tinubu; Shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari, Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan Nasarawa, Abdullahi Adamu; Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal; Shugaban hukumar NTDC, Folarin Coker; Ministan Sadarwa, Lai Mohammed.

Cikin jerin sunayen akwai hafsin sojin Najeriya, Laftanat Tukur Buratai; Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika; Mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari; Shugaban hukumar tace fina-finai na kasa, Adedayo Thomas; Tsohon gwamnan Bauchi, Adamu Mu'azu; Tsohon gwamnan jihar Osun, Iyiola Omisore; Tsohon shugaban hukumar Fanso na kasa, Abdulrashin Maina; Tsohon karamin Ministan Tsaro, Musliu Obanikoro da Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu.

Saura sun hada da Gwaman Bauchi, Isah Yuguda; Sanata Godswill Akpabio; Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbanjo; Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje; Tsohon gwamna jihar Jigawa, Saminu Turaki, Sakataren BCDA kuma surukin Buhari, Junaid Abdullahi; tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Wamako; Dan takarar gwamnan APC na jihar Imo, Hope Uzodinma, Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi da gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

Har ila yau, sauran wadanda aka ambaci sunayensu su ne, Shugaban hukumar NNPC, Maikanti Baru da Shugaban hukumar tattara bayannan sirri na kasa (NIA) da aka dakatar, Ayodele Oke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel