Kungiyar Darul Hadeeth za ta marawa Buhari da El-Rufai baya a zaben 2019
Mun ji labari cewa an samu wata kungiyar addinin musulunci da ke Arewacin Najeriya ta fito ta nuna goyon bayan ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a wannan zaben da za ayi kwanan nan.

Asali: UGC
Kungiyar nan ta Darul Hadeeth Salafiyyah da ke Zaria za ta marawa shugaba Buhari baya a zaben 2019. Kungiyar ta kuma jadaada goyon bayan ta ga ‘dan takarar gwamnan jihar Kaduna jam’iyyar APC watau Malam Nasir El-Rufai.
Darul Hadeeth Salafiyyah ta nuna cewa Muhammadu Buhari ne ‘dan takarar da ya fi cancanta a zaba a 2019 domin cigaba da gyara Najeriya. A cewar kungiyar, an muzgunawa addinin musulunci a lokaci gwamnatocin PDP a kasar.
KU KARANTA: Gwamna Wike ya ajiye banbanci ya nemi jama’a su marawa Atiku baya
Dr. Abdurrafi Abdulganiyy wanda shi ne shugaban wannan katafariyar kungiyar ya bada tabbacin cewa dinbin Mabiyan su za su goyawa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da kuma shugaba Muhammadu Buhari baya.
A gwamnatin PDP ne dai kungiyar ta Darul Hadeeth Salafiyyah wanda tayi fice ta rasa babban Malamin ta kuma wanda ya kafa ta watau Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani wanda ‘yan bindiga su ka budawa wuta cikin dare.
Jiya kun ji kishin-kishin din cewa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya rabawa shugaban kungiyar Izala na kasa wasu sababbin motoci kwanan nan. Kungiyar Izala dai ta karyata wannan zance tuni.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng