Mata ta kone mijinta kurmus saboda ya ki yarda ta duba wayarsa, hoto

Mata ta kone mijinta kurmus saboda ya ki yarda ta duba wayarsa, hoto

- Jami'an tsaro sun kama wata mace mai shekaru 25 mai suna Ilham Chayani saboda laifin cinna wa mijinta wuta da ransa

- A cewar rahoton, matar da cinna wa mijinta wuta ne saboda ya ki bata lambar sirrin bude wayarsa na salula

- Mijin nata, Dedi Purnama mai shekaru 26 ya rasu a asibiti kwanaki biyu bayan afkuwar lamarin a Yammacin Nusa Tenggara a Indonesia

Sabanni tsakanin mutane musamman ma'aurata abu ne wanda ke faruwa daga lokaci zuwa lokaci, shiyasa masu iya magana su kan ce 'Zo mu zauna, zo mu saba' sai dai abinda ke da muhimmanci shine hanyoyin da ake bi wurin warware matsalolin ba tare da cutar da juna ba.

Dedi Purnama mai shekaru 26 ya hau sama yana gyran rufin gidansu ne sai matarsa mai shekaru 25 ta bukaci ya fada mata lambar sirri na bude wayansa wato 'Password' amma ya hana ta. Hakan yasa rikici ya barke tsakaninsu.

Daga bisani rikicin ya kazanta har ta kai mijin ya saka hannu ya doke ta. Bayan haka sai ta watsa matsa fetur ta cinna masa wuta.

Mata ta kone mijinta kurmus saboda ya ki yarda ta duba wayarsa, hoto
Mata ta kone mijinta kurmus saboda ya ki yarda ta duba wayarsa, hoto
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya fadi dalilan da yasa har yanzu ake da almajirai a Najeriya

Mata ta kone mijinta kurmus saboda ya ki yarda ta duba wayarsa, hoto
Mata ta kone mijinta kurmus saboda ya ki yarda ta duba wayarsa, hoto
Asali: Twitter

Purnama ya rasu kwanaki biyu bayan afkuwar wannan lamarin a wani asibiti da ke yankin West Nusa Tenggara na kasar Indonesia.

Wani wanda ya shaida faruwar lamari, Oti ya fadawa kafafen watsa labarai na kasar cewa ya garzaya zuwa gidan ma'auratan a yayin da ya ga wuta ta tashi a gidan domin ya taya su kashe wutar.

Rahotanni sun ce tuni 'yan sanda sun damke Cahyani kuma ana tsare da ita a ofishin 'yan sanda na Gabashin Lombok sai dai babu san ko an tuhume ta da wani laifi ba a halin yanzu.

Har yanzu dai ana gudanar da bincike ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel