Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 2

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 2

- Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomin Gagarawa da Kaugama

- Alhaji Ibrahim Kudaita, shugaban kwamitin, ya zargi shugabannin kananan hukumomin da kawo wa aikin kwamitinsa cikas ta hanyar kin zama a ofis

- Majalisar ta umarci shugabannin kananan hukumomin su mika mulki ga mataimakansu domin cigaba da gudanar da aiyuka a hukumance

A jiya, Laraba, ne majalisar dokokin jihar Jigawa ta sanar da dakatar da wasu shugabannin kananan hukumomi biyu saboda rashin samun su a ofis lokacin da mambobin majalisar su ka ziyarar aiki kananan hukumominsu.

Shugabannin kananan hukumomin su ne Mallam Ibrahim Ya', shugaban karamar hukumar Gagarawa da takwaransa Alhaji Ahmad Marke, shugaban karamar hukumar Kaugama.

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 2
Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru Talamiz
Asali: Depositphotos

An dakatar da shugabannin kananan hukumomin ne bayan kwamitin kula da kananan hukumomi ya gabatar da wani rahoto a kan ziyarar da su ka kai kananan hukumomin jihar Jigawa a gaban ragowar mambobin majalisar. Mambobin kwamitin sun ce ba su samu shugabannin kananan hukumomin a ofishinsu ba lokacin da suka kai ziyarar aiki.

DUBA WANNAN: Zan azurta abokaina idan na zama shugaban kasa - Atiku

Alhaji Ibrahim Kudaita, shugaban kwamitin, ya zargi shugabannin kananan hukumomin da kawo wa aikin kwamitinsa cikas, lamarin da ya ce ya saba da sashe na 9 na kundin dokokin kananan na shekarar 2012.

Majalisar ta umarci shugabannin kananan hukumomin su mika mulki ga mataimakansu domin cigaba da gudanar da aiyuka a hukumance.

Alhaji Muhammad Ahmed Garba, mataimakin shugaban majalisar, ne ya fara sanar da bukatar dakatar da shugabannin kananan hukumomin, sannan ragowar mambobin jam'iyyar suka mara ma sa baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng