Kamfen: Aisha Buhari za ta ziyarci jihar Bauchi a yau
Mun samu rahoton cewa mai dakin shugaban kasa, Mrs Aisha Buhari za ta kai ziyara jihar Bauchi a yau.
Daily Trust ta ruwaito cewa za ta kai ziyarar ne domin yiwa mijinta, shugaba Muhammadu Buhari kamfen a yunkurinsa na neman sake zarcewa a kan mulki karo na biyu a babban zaben 2019.
Ana sa ran za ta hallarci wani taron jin ra'ayin mutane tare da kungiyoyin mata daban-daban a jihar ta Bauchi.
Majiyar Legit.ng ta gano cewa matar mataimakin shugaban kasa, Mrs Dolapo Osinbajo ne za ta wakilic Aisha Buhari a wurin taron.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: 'Yan PDP fiye da 1,000 sun koma APC a garinsu Gwamna Tambuwal
A wani rahoton kuma, Legit.ng ta kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin Lokoja na jihar Kogi inda zai gana da yan jam’iyyar APC da magoya bayansa a yayin da zai kaddamar yakin neman zabensa a jahar.
Legit.ng ta ruwaito da misalin karfe sha biyu da yan mintoci jirgin Buhari ya tashi daga fadar shugaban kasa, sai dai irin jirgin nan ne da ake kira da suna ‘Mai saukan Angulu’, a cikinsa ne Buhari nufi garin Lokoja
Kazalika, Buhari ya soke zuwa garin Ilorin na jahar Kwara sakamakon fasa gudanar da yakin neman zaben nasa a yau da jam’iyyar APC ta yi, APC ta fasa gudanar da yakin neman zaben ne biyo bayan rikicin daya barke yayin da wasu yan jagaliya suka afka ma gidan Sanata Bukola Saraki.
An yi asarar rayuka da dukiyoyi a yayin wannan rikici daya barke tsakanin magoya bayan Saraki da abokan hamayyarsa, wannan takaddama yasa gwamnatin jahar ta saka dokar ta baci akan duk wani gangamin siyasa a fadin jahar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng