Jirgin yakin PDP ya danna kasar Yarabawa, Ile-Ife ta dauki dumi da saukar Turaki wazirin Adamawa
- Dan takarar shugabancin kasa a jam'iyar PDP Atiku Abubakar yakai ziyarar yada manufa masarautar Ooni ta Ife
- Atiku ya samu rakiyar matar sa Titi zuwa wannan masarauta
- Yace yakai wannan ziyara ne don nuna girmamawa ga masarautar ta Ile Ife

Source: Twitter
Dan takarar shugabancin kasa a jam'iyar PDP Atiku Abubakar yakai ziyarar yada manufa a masarautar Ooni dake Ife.
Atikun ya kai wannan ziyara ne a ranar Talata inda ya samu rakiyar matarsa Titi, tsohon gwamnan jihar Osun, ciyaman na jam'iyar PDP da kuma tsohon gwamnan jihar Ogun.

Source: Twitter
Da yake magana a masarautar Atiku yace "Mun kawo wannan ziyara ne don nuna girmamawa ga wannan masarauta ta Ile Ife."
"Ile Ife tana daya daga cikin wani jinsi na Yoruba wadanda suke da karfi a fadin Najeriya saboda haka muka kawo musu ziyarar girmamawa".
"Sannan ina mika godiya ta ga Ooni, chief da sauran al'ummar wannan waje bisa goyan baya da suka bamu."
GA WANNAN: Hodijam! Saraki ya gwale IGP guda dazunnan a filin faretin tunawa da Soji
Da yake tofa albarkacin bakin sa Sarkin Oba Adeyeye ya janyo hankalin yan siyasa dasu sanya Najeriya sama da wasu bukatun su a zabe mai zuwa na shekara ta 2019.
"Ya zama dole mu sanya Najeriya sama da komai."
Duk da kasancewar mu yan kasa daya ya zama dole mu kore duk wani abu dazai kawo mana hargitsi akan siyasa.
GA WANNAN: Hukumar 'Yansanda ta tabbatar wa Najeriya zata sanya ido sosai kan yadda ma'aikatanta zasu yi aiki lokutan zabe
PDP dai na matukar bukatar wannan yanki na Yarabawa mai yawan kuri'u, kuma akwai alamun ta fara samun tagomashi tun lokacin da aka yi zabukan Ekiti da Osun, APC ta sha da kyar, lamari da ya nuna lallai ko ana iya cewa Bola Tinubu na da karfi to kau lallai ba kowa ke bin sa sau da kafa ba.
Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa
Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng