Mun cire sunayen kananan yara daga cikin rajistan zabe - INEC
- Hukumar INEC ta sanar da cewa ta cire sunayen mutanen da shekarunsu bai kai na jefa kuri'a ba daga rajistan ta
- Wannan ya biyo bayan korafe-korafen da aka rika yi ne a zabukkan da suka gabata inda aka ruwaito cewa yara kanana sun kada kuri'u a wasu zabukkan
- Hukumar Zaben ta ce a shirye ta ke domin gudanar da tsaftacecen zabe mai inganci da al'umma za suyi na'am dashi
Kimanin wata daya da ya wuce, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar da cewa ta tsaftace sunayen masu kada kuri'a ta hanyar cire sunayen kananan yara da ba su kai shekarun zabe ba domin tabbatar da anyi tsaftatacen zabe mai inganci a 2019.
Hakan na kunshe ne cikin jawabin da Kwamishinan INEC na jihar Kaduna, Abdullahi Kaigama ya yi yayin wata taron musayar ra'ayoyi da shugabanin addinai a ranar Talata a Kaduna.
Kaigama ya ce hukumar na da babban aiki a gabanta musamman yanzu da zaben ya matso kusa.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Legas: An kama manyan 'yan kasuwa dake daukar nauyin 'yan bindigar Zamfara
"Da hadin kan masu ruwa da tsaki, tabbas za muyi zaben cikin nasara," inji shi.
Ya yi kira da dukkan masu kada kuri'a da basu karba katin zabensu na dindindin ba su garzaya su karba a tsakanin ranakun 16 da 21 na watan Janairun shekarar 2019 a mazabobinsu.
Kaigama ya ce alkalluman da hukumar ke da shi a yanzu ya nuna mutanen da su kayi rajitsa sun kai 84,004,084.
Ya ce da wadannan sunayen ne za ayi amfani a rumfunan zabe a sassan kasar nan.
A cewarsa, "Bayan ranar 21 ga watan Janairu, duk wanda bai karba katin zabensa ba sai ya tafi ofisoshin hukumar da ke kananan hukumomi ya karba har zuwa ranar 8 ga watan Fabrairun 2019."
A yayin da ya yabawa shirye-shiryen da INEC tayi game da zaben, Shugaban CAN na reshen jihar Kaduna, Rev. John Joseph Hayab ya kallubalanci INEC ta aiwatar da abubuwan da ta fada idan lokacin zabe ya yi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng