Manyan APC sun taya Bisi Akande murnar cika shekara 80 da haihuwa

Manyan APC sun taya Bisi Akande murnar cika shekara 80 da haihuwa

Mun samu labari cewa manyan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun taya Bisi Akande murnar cika shekara 80 a Duniya. Cif Bisi Akande shi ne shugaban APC na farko da aka yi bayan kafa jam’iyyar a 2013.

Manyan APC sun taya Bisi Akande murnar cika shekara 80 da haihuwa
Bisi Akande shugaban jam’iyyar APC na farko ya cika shekaru 80
Asali: Depositphotos

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma sauran jagororin APC irin su Bola Ahmed Tinubu da Kayode Fayemi sun gaida Bisi Akande murnar cika shekaru 80 da haihuwa. Cif Akande ya rike Gwamnan jihar Osun a 1999.

Shugaba Buhari yace hangen nesan Akande yana cikin abin da ya sa jam’iyyar APC ta doke PDP a zaben 2015. A wancan lokaci ne karon farko da jam’iyyar hamayya ta hambarar da gwamnati mai ci a tarihin siyasar Najeriya.

KU KARANTA: Shugabannin APC a Kaduna sun yi wa Buhari alkawarin kuri'u 90%

Femi Adesina wanda ke magana da yawun Buhari ya fitar da wannan jawabi a jiya. Shugaban kasar ya kara da cewa siyasar Najeriya ta ci moriyar Bisi Akande inda ya kara addu’a ga Ubangiji ya kara masa nisa da tsawon kwana.

Tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu, wanda jigo ne a APC ya bayyana Bisi Akande a matsayin mutumin kirki na kin karawa. Bola Tinubu yace tsohon shugaban na APC, abin koyi ne ga mutanen baya masu tasowa a kasar.

Shi ma gwamnan jihar Ekiti kuma tsohon Ministan Buhari watau Dr. Kayode Fayemi ya jinjinawa Dattijon wanda ya kira Mai gidan sa. Fayemi godewa Ubangiji da yayi aiki a karkashin wannan Bawan Allah mai matukar hakuri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel