Mutuwar Sarkin Lafiya: Kalli wasu mutane 10 dake gwagwarmayar maye gurbinsa

Mutuwar Sarkin Lafiya: Kalli wasu mutane 10 dake gwagwarmayar maye gurbinsa

Kimanin kwanaki hudu kenan tun bayan rasuwar mai martaba sarkin Lafiya, Alhaji Isa Mustapha Agawai I, tuni har yayan Sarki sun fara gogoriyon maye gurbinsa tare da ganin kowannensu ya kai bantensa a kokarin ganin ya zama Sarki na goma sha bakwai.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin wadanda suka shahara wajen neman zama Sarkin Lafiya akwai yayan Sarki guda Arba’in da bakwai, wadanda wadand ke kan gaba a wannan gwagwarmaya da ake tunanin tantancesu guda shida ne, sune;

KU KARANTA; Kungiyar Izala ta bayyana sunan wanda take goyon baya a zaben shugaban kasa na 2019

Mutuwar Sarkin Lafiya: Kalli wasu mutane 9 dake gwagwarmayar sun maye gurbinsa

Marigayi
Source: UGC

1- Alhaji Isiyaku Dauda Madakin Lafiya

2- Mai Sharia Sidi Ali na kotun daukaka kara

3- Musa Isa Mustapha Ubangarin Lafiya

4- Alhaji Abdullahi Yusuf Musa babban sakatare a ma’ikatar ilimi ta jahar Nassarawa

5- Alhaji Aminu Kachallan Lafiya

6- Alhaji Muhammad Moyi Maidunama

Sauran sun hada da Umar Sanda, Musa Dan Jaji, Lamino da Musa Gana, ana sa ran daga cikin wadannan sa sauran masu neman sarautar guda Talatin da bakwai ne za’a mika sunayensu ga masu nadin Sarki, sai dai daga gidajen sarautar Ari da Dal lake sa ran fitowar sabon Sarki.

Mutane biyar da hakkin zaban sabon Saraki ya rataya a wuyansu sun hada da Makongiji, Salanke, Moyi, Sarkin fada da kuma babban limamin gari, wadanda sune zasu tantance yan takarkarun, daga nan sai su mika sunayen ga ma’aikatar kananan hukumomi, zuwa gwamnan jahar da kuma majalisar sarakunan gargajiya ta jahar don zaban wanda ya fi cancanta.

A ranar da aka gudanar da addu’an sadakar uku an hangi Sarkin Kazaure, Sarkin Dass, Wamban Kano, Sarkin Bauchi da sauran hakiman masarautar Lafiya sun shiga wata ganawa da yayan Sarki mai rasuwa, inda suka kwashe awanni suna tattaunawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel