Ka daina yiwa Buhari sharri - Fadar shugaban kasa ta gargadi Ortom

Ka daina yiwa Buhari sharri - Fadar shugaban kasa ta gargadi Ortom

Fadar shugaban kasa tayi kira ga gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, da ya mayar da hankali a kan kokarin warware matsalolin da jihar sa ke ciki, ba ya dinga yawo yana yada karya a kan shugaba Buhari ba.

A sanarwar da Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari, ya fitar, ya ce, "muna da masaniyar cewar gwamna Ortom na ziyartar Cocin jihar sa tare da fadawa jama'a cewa shugaba Buhari nada shirin musuluntar da Najeriya.

"Da wannan zance na shirme yake yawo yana yakin neman zabe saboda bashi da abinda zai nuna a matsayin aikin da ya yiwa jama'a.

"Rashin adalci ne ga gwamna Ortom ya fadi haka a kan Buhari, musamman idan aka yi la'akari da irin goyon baya da gudunmawa da ya samu daga gwamnatin tarayya lokacin da rigingimu makiyaya da manoma suka addabi jihar Benuwe," kamar yadda jawabin ya kunsa.

Ka daina yiwa Buhari sharri - Fadar shugaban kasa ta gargadi Ortom
Buhari da Ortom
Asali: Depositphotos

Jawabin ya kara da cewa, "ba don goyon bayan shugaba Buhari a kan a bar Ortom ya kawo duk tsarin da yake so a Benuwe ba, da bai sukunin kaddamar da dokokin da ya kirkira ba."

DUBA WANNAN: Ministan Buhari ya bayyana irin mawuyacin hali da PDP ke ciki

Kazalika fadar ta shugaban kasa ta gargadi Ortom da ya guji yiwa Buhari sharri tare da yin kira ga jama'ar jihar Benuwe da kar su bari ya yaudare su da wadannan karairayi.

"Ku tambaye shi me yasa ya kasa biyan albashin ma'aikata da kudin 'yan fansho da kuma abinda ya yi da kudin rarar danyen mai da ya karba daga gwamnatin tarayya," a cewar jawabin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel