Kudan Zuma ya tashi al'ummar garin Gunsun na jihar Filato

Kudan Zuma ya tashi al'ummar garin Gunsun na jihar Filato

Da sanadin kafar watsa labarai ta BBC Hausa mun samu rahoton cewa, ba bu zato ba bu tsammani curi na garken Kudan Zuma sun fatattaki al'ummar kauyen Gunsun da ke karkashin karamar hukumar Kanam ta jihar Filato.

Kamar yadda Sarkin Gunsun Idris Muhammad ya shaidawa manema labarai, lamarin ya afku ne da tsakar ranar yau ta Lahadi, inda ba bu zato ba bu tsammani curi na Kudajen Zuma suka mamaye kauyen baki daya.

Nan take cikin neman tsira da kuma mafaka, al'ummar kauyen suka tarwatse inda suka bazama cikin dajika ba tare da sanin inda suka dosa ba. Mutane dama sun raunata yayin neman tsira yayin da ta kai wasun su ga karaya ta kashi.

Kudan Zuma ya tashi al'ummar garin Gunsun na jihar Filato
Kudan Zuma ya tashi al'ummar garin Gunsun na jihar Filato
Asali: UGC

Ya ke cewa, an taki babbar sa'a da ba bu ko rai guda da ya salwanta a sakamakon yadda firgici da kuma dimuwa ta sanya kowa ya yi ta kansa zuwa dokar daji.

Cikin jawaban da ya shaidawa manema labarai, wani mazaunin garin mai sunan Ibrahim, ya ce aukuwa wannan annoba ta bazata ta yiwa dabbobin su da dama lahani.

KARANTA KUMA: Makiyaya sun yiwa Masunta mummunan ta'addanci a jihar Delta

Ana zargin takalar yaran kauyen ta sanya wannan garke na Kudan Zuma su ka afko cikin al'umma daga jikin wani Itacen Rimi dake bayan gari. Kazalika wasun su na zargin Kudan Zuman jifa ne irin na asararu.

Tarihi ya bayyana cewa, makamancin wannan lamari ya taba faruwa cikin kauyen na Gunsu a shekarar 1998 inda aka samu asarar rayuka kamar yadda Sarki Idris ya bayyana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel