Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PPC ya sha alwashin lallasa Buhari da Atiku a zaben 2019

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PPC ya sha alwashin lallasa Buhari da Atiku a zaben 2019

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Providence Peoples Congress (PPC), Mista Victor Okhai, ya sha alwashin lallasa dan takara na jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma na babbar jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar a zaben 2019.

A jiya Asabar dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PPC, Mista Victor Okhai, ya lashi takobin cin galaba akan dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuma na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari a babban zaben kasa da za a gudanar cikin watan Fabrairu na gobe.

Okhai ya yi wannan bugun gaba yayin yakin neman jam'iyyar sa da aka gudanar cikin birnin Ibadan na jihar Oyo, inda ya ce daga shekarar 1999 kawowa yanzu ba bu abinda dimokuradiyya ta tsinana na ci gaban al'ummar kasar nan.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PPC ya sha alwashin lallasa Buhari da Atiku a zaben 2019

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PPC ya sha alwashin lallasa Buhari da Atiku a zaben 2019
Source: Depositphotos

Ya ke cewa, jam'iyyar sa ta PPC na da duk wata nagarta da cancanta da samun nasarar kujerar shugaban kasa da kuma kujerun gwamnoni na mafi akasarin jihohin kasar nan a yayin babban zabe.

A sanadiyar haka Okhai ya ke kira da kuma gargadi ga al'ummar kasar nan kan fitowa kwansu da kwarkwata domin kwatar 'yancin su wajen hukunta jam'iyyar APC da kuma ta PDP da suka dakusar da ci gaban Najeriya.

KARANTA KUMA: Tsanani a Najeriya ba zai yanke ba muddin aka sake zaben Buhari - Babban Fasto

Cikin zayyana jawaban sa, dan takarar kujerar gwamnan jihar Oyo na jam'iyyar PPC, Mista Taiwo Otegbeye, da ya kasance tsohon kwamishinan labarai na jihar, ya ce jam'iyyar sa za ta tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya wajen yaye kangi na talauci da ya yiwa al'umma katutu.

Otegbeye ya kuma sha alwashin kawo managarcin sauyi na bunkasa da kuma habakar ci gaba na jin dadin al'ummar jihar ta fuskar harkokin ilimi, tattalin arziki, noma, kiwon lafiya da makamantan su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel