Yaron nan da ya sayar da kodarsa don sayen iPhone a 2011 na can yana bukatar koda

Yaron nan da ya sayar da kodarsa don sayen iPhone a 2011 na can yana bukatar koda

- Saurayin da ya siyar da kodar shi na nan kwance rai a hannun Allah

- Ya siyar da kodar ne don ya siya iPad da IPhone a 2011

- Yanzu haka yana dogaro da wankin koda ne don rayuwa

Yaron nan da ya sayar da kodarsa don sayen iPhone a 2011 na can yana bukatar koda

Yaron nan da ya sayar da kodarsa don sayen iPhone a 2011 na can yana bukatar koda
Source: Facebook

Wani matashi wanda ya siyar da kodar shi don siyan iPhone da ipad na nan a nakashe, kwance rai a hannun Allah sakamakon ciwon dayar kodar.

Saurayin dan shekaru 17 a shekarar 2011 ya siyar da kodar shi don ya nuna ma abokan shi shima ya shigo gari.

Yaron nan da ya sayar da kodarsa don sayen iPhone a 2011 na can yana bukatar koda

Yaron nan da ya sayar da kodarsa don sayen iPhone a 2011 na can yana bukatar koda
Source: Facebook

Ya hadu da wasu mutane uku ne a kafar sadarwa in da ya bayyana musu kudurin shi, su kuma suka ce zasu taimake shi.

A lokacin saurayin ya bar gidan iyayen shi dake gabashin yankin Anhui zuwa kudancin yankin a watan Afirilu na 2011.

Yaron nan da ya sayar da kodarsa don sayen iPhone a 2011 na can yana bukatar koda

Yaron nan da ya sayar da kodarsa don sayen iPhone a 2011 na can yana bukatar koda
Source: UGC

Ya shirya tafiyar a asirce ba tare da sanin iyayen shi ba. Da isar shi mutanen suka hada shi da wasu likitocin fida biyu, mataimaki daya da wata malamar jinya wadanda sukayi aikin cire kodar.

An siyar da kodar ba bisa ka'ida ba a Yuan 150,000 dai dai da £17,258 da kuma dala 10,000 dai dai da £7,860. Amma sai suka ba saurayin kashi goma na kudin daidai da yuan 22,000 ,£2,528.

Saurayin yayi maza ya siyo iPhone 4 da iPad 2 da kudin kafin ya koma gida.

Mahaifiyar shi ta gano halin da ake ciki ne bayan da ta ganshi dasu. Wangg ya sanar da ita ya siyar da kodar shi in da a take ta kira yan sanda.

A watan Afirilu na 2012 ne aka yankewa mutane 9 da ke da hannu a cikin cire kodar hukunci.

GA WANNAN: An kammala wasu sabbin tashoshin lantarki 8 da biliyoyin kudi ana dab da zabe

Mutanen uku an yanke musu shekaru 3 zuwa 5 a gidan kaso, sai likitocin kuma shekaru 3 kowanne a gidan kaso.

An biya dangin Wangg-yuan miliyan 1.47 dai dai da £169,000 (N84,900,000) kamar yanda kotu ta umarta.

Saurayin wanda yanzu ya kara girma na nan kwance inda dangin shi ke kula da shi don ciwon koda da ke damun shi.

Ya bar karatun shi a halin yanzu don yana dogaro ne da wankin koda.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel