Lafiya Jari: Amfanin Kokwamba ga lafiyar Dan Adam

Lafiya Jari: Amfanin Kokwamba ga lafiyar Dan Adam

Cin abinci da dare gabanin kwanciyar bacci abu ne wanda likitoci suke jan kunne a kai duba da tarin illolin yin hakan. Bayan wasu gwaje-gwaje an gano cewa idan baza ka iya hakuri da cin abincin ba to kaci kwakwamba a mai makon abinci mai maiko.

Kokwamba tana daya daga cikin dangin ya'yan Duma mafi shahara a duniya sakamakon tasirin ta na inganta lafiyar jikin bil'adama duba da irin sinadaran da take kunshe dasu, kama daga Polyphenols, Lignans, Fibre, Vitamin K, Potassium da makamantan su.

Lafiya Jari: Amfanin Kokwamba ga lafiyar Dan Adam

Lafiya Jari: Amfanin Kokwamba ga lafiyar Dan Adam
Source: UGC

Kwakwamba tana kunshe da kimanin kaso 95 bisa 100 na ruwa wanda jikin dan Adam yake bukata domin kawar da dattin jiki ko maiko. Tana kuma kunshe da sinadarai wanda ke kawar da yunwa da wuri da za ta rage kwalamar ciye-ciyen maiko ga mutum gabanin kwanciyar bacci.

Wani muhimmancin cin kwakwamba da daddare shi ne tana rage hadarin kamuwa da ciwon kai ko fargabar dare domin tana kunshe da sinadari masu inganta bacci.

A fannin lafiyar maza kuma, kwakwamba tana karawa namiji kuzari, da hakan yake samuwa sakamakon wasu sinadarai masu inganta karfin mazakuta.

KARANTA KUMA: Saboda Buhari aka samu rangwamin tsanani a Arewa maso Gabas - Okorocha

A fannin lafiyar mata, kwakwamba tana taimakawa kwarai da aniyya wajen gyara fata musamman fuska domin kuwa ta kunshe da sinadari mai tsotse kwayoyin cututtuka na bakteriya (Bacteria) a jikin mata.

Baya ga inganta lafiya gani ta hanyar karfin idanu, ko shakka ba bu binciken masana kiwon lafiya ya tabbatar da cewa, Kokwamba ta na da tasirin gaske wajen yakar cututtuka musamman ciwon daji wato Cancer a turance da kuma cutar hawan jin mai sanya bugun zuciya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel