Ali Nuhu da Rara sun halarci kaddamar da kamfen din gwamnan APC a arewa

Ali Nuhu da Rara sun halarci kaddamar da kamfen din gwamnan APC a arewa

- A jiya, Litinin, ne gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, ya kaddamar da yakin neman zabensa

- Yakin neman zaben da aka kaddamar a Ribadu Square ya samu halartar manyan 'yan siyasar jihar Adamawa

- Gwamna Bindow na fuskantar adawa mai karfi daga cikin jam'iyyar APC bisa zarginsa cogen takardun karatu

Sati biyu bayan 'yan takarar gwamnan a jam'iyyun PDP, Umaru Fintiri, da SDP, Emmanuel Bello, sun kaddamar da yakin neman zabensu, gwamna Jibrilla Bindow na jihar Adamawa ya kaddamar da nasa kamfen din a jiya, Litinin.

Yakin neman zaben da aka kaddamar a Ribadu Square dake Jimeta a garin Yola ta samu halartar manyan jaruman masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood).

Fitattu daga jaruman Kannywood da suka halarci sun hada da Ali Nuhu da Dauda Kahutu Rara.

Ali Nuhu da Rara sun halarci kaddamar da kamfen din gwamnan APC a arewa
Ali Nuhu da Rara sun halarci kaddamar da kamfen din gwamnan APC a arewa
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Sunaye: Manyan jaruman Kannywood dake cikin kwamitin kamfen din Aisha

Ana kyautata zaton Bindow zai lashe zaben gwamnan Adamawa cikin sauki bisa dogaro da farin jinin da yake da shi a jihar saboda aiyukan da ya yiwa jama'a.

Sai dai har yanzu Bindow na fuskantar adawa daga cikin jam'iyyar APC a wurin abokan takarar sa, Nuhu Ribadu da Ahmed Halilu (Modi) da suka fafata a zaben fidda 'yan takara da aka yi a watan Oktoba na shekarar da ta kare.

Ribadu da Modi na zargin saba dokokin jam'iyya a zaben da ya samar da Bindow a matsayin dan takarar gwamna a karo na biyu.

Duk da adawar da Bindow ke fuskanta daga manyan 'yan siyasar biyu, masu alhakin yi masa yakin neman zaben na ganin cewar hakan ba zai hana shi samun nasara a zaben da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel