'Yan sanda sun kashe kasurgumin dan fashi a jihar Katsina

'Yan sanda sun kashe kasurgumin dan fashi a jihar Katsina

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta sanar da mutuwar wani kasurgumin dan fashi, Kane Mohammed, da aka fi sani da 'Dan mai-keke'.

Wannnan sanarwa na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya bawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a yau, Lahadi.

Isa ya bayyana cewar jami'an rundunar 'yan sanda sun kashe kasurgumin dan fashin ne a ranar 4 ga watan Janairu yayin wani samame a maboyar 'yan ta'adda a yankin karamar hukumar Bakori.

A cewar kakakin, 'yan ta'addar ne suka fara kai wa tawagar jami'an 'yan sanda hari da muggan makamai har ta kai ga sun raunata dan sanda guda.

'Yan sanda sun kashe kasurgumin dan fashi a jihar Katsina
Jimoh Moshood, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa
Asali: Facebook

Ya kara da cewar shugaban 'yan fashin ya mutu ne a asibitin garin Bakori, inda jami'an 'yan sanda suka garzaya da shi bayan samun rauni daga harbin bindiga yayin arangama da 'yan fashin.

Kazalika ya bayyana cewar suna cigaba da gudanar da bincike domin kama ragowar 'yan tawagar Dan mai-keke'.

DUBA WANNAN: Sojoji sun yi dirar mikiya ofishin Daily Trust a Maiduguri, sun awon gaba da Edita

Ko a ranar ranar Laraba da ta gabata saida Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya sanar da cewa 'yan ta'adda sun mamaye sassa da dama na jihar a wurin taron gaggawa na masu ruwa tsaki a fanin tsaro inda ya ce mutanen jihar sunan cikin hadari har ma da shi.

A yayin da ya ke yiwa manema labarai bayanin wasu abubuwan da aka tattauwa wurin taron, sakataren gwamnatin jihar, Fr. Mustapha Mohammed Inuwa ya gargadin cewa akwai yiwuwar ba za ayi zabe a kananan hukumomi 8 ba muddin ba a dauki mataki ba kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Kananan hukumomin da ya ce 'yan ta'adda da barayin shanu sun mamaye a jihar sun hada da Jibia, Batsari, Safana, Dan-Musa, Faskari, Sabuwa, Dandume, Kankara da wasu sassan Kafur wadda itace karamar hukumar da gwamna ya fito daga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel