Matasa: Ku fara shirin rike akalar jagoranci - Buhari

Matasa: Ku fara shirin rike akalar jagoranci - Buhari

A yau Juma'a shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kirayi matasan Najeriya akan su fara yiwa kawunan su tanadi da horo na rike akalar jagoranci domin kuwa nan ba da jimawa ba za su ci gajiyar karagar mulki da jagoranci irin na siyasa.

Shugaban kasa Buhari ya bayyana haka ne yayin karbar bakuncin kungiyar Matasan kabilar Yarbawa ta Ndigbo, inda mukaddashin shugaban kungiyar, Kingsley Dozie Lawrence, ya jagoranci tawaga har zuwa fadar Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Shugaba Buhari ya zayyana yadda muhimmancin Matasa ya kasance wannan babban jigo kuma ginshiki mai tasirin gaske wajen assasa tubali na kyakkyawar makoma da ci gaban kasa kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Matasa: Ku fara shirin rike akalar jagoranci - Buhari

Matasa: Ku fara shirin rike akalar jagoranci - Buhari
Source: Twitter

Ya ke cewa, ba dade ko ba jima, matasa za su karbi ragamar jagorancin kasar nan da tun a yanzu ya kamata su kasance cikin shiri da daura damarar horad da kawunan su akan nauyin da zai rataya a wuyan su.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito, shugaba Buhari ya yi makamancin wannan furuci yayin karbar bakuncin kungiyar daliban Najeriya ta NANS yayin da ziyarci fadar sa a jiya Alhamis.

KARANTA KUMA: Sufeto Janar ya mayar da mukamin Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Imo

Kazalika, shugaban kasa Buhari ya yi jinjina ga kungiyar Matasan dangane da yabawa kwazo da bajintar gwamnatin sa wajen tabbatar da kyakkyawan ci gaba da kasar nan ta ke matukar muradi a halin yanzu.

Shugaban kasar ya kuma kyautata zaton sa dangane da yunkurin gwamnatin tarayya na sulhuntawa tsakanin ta da kungiyar Malaman jami'o'in Najeriya da ta ke ci gaba da tayar da kayar baya na yajin aiki da ta afka tsawon watanni biyu da suka gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel