Obasanjo da Jonathan za su rabauta da babban kaso na N2.3bn cikin kasafin kudin 2019

Obasanjo da Jonathan za su rabauta da babban kaso na N2.3bn cikin kasafin kudin 2019

A ranar Laraba, 19 ga watan Dasumba na shekarar 2018 da ta gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gabatar da kasafin kudin kasar nan na shekarar 2019 da ya kai kimanin Naira tiriliyan 8.83 a zauren majalisar dokoki ta tarayya.

Kamar yadda doka tayi tanadi, dole akwai wani hasafi na dukiya da gwamnatin kasa ke fitarwa ga shugabanninta da suka shude matukar su na raye sakamakon bauta da suka yiwa kasar su a lokacin da suke kan karagar mulki.

A sanadiyar haka mun samu cewa, tsaffin shugabannin Najeriya da suka hadar da Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan da kuma shugabannin ma'aikatan su a yayin jagorancin kasa, za su rabauta da hasafin Naira biliyan 2.3 kamar yadda kasafin kudin 2019 ya yi tanadi.

Obasanjo da Jonathan za su rabauta da babban kaso na N2.3bn cikin kasafin kudin 2019
Obasanjo da Jonathan za su rabauta da babban kaso na N2.3bn cikin kasafin kudin 2019
Asali: UGC

Kazalika akwai kimanin Naira biliyan 4.5 na hasafi da tsaffin shugabannin ma'aikata da kuma tsaffin sakatarori na dindindin na gwamnatin tarayya za su rabauta, yayin da tsaffin shugabannin cibiyoyi da ma'aikatun gwamnati za su rabauta da Naira biliyan 1 na hasafi dangane da hidima da su ka yiwa al'ummar kasa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan tanadi na hasafi ya yi daidai da tsare-tsare da ke cikin kasafin kudin kasa na shekarar 2019 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabata a zauren Majalisar dokoki ta tarayya makonnin kadan da suka gabata.

KARANTA KUMA: Sabuwar Shekara: Buhari ya fifita Kiristoci a kan Musulmai - MURIC

Gwamnatin tarayya ta kuma tanadi Naira biliyan 75 domin duk wata gudanar ta hukumar sojin Najeriya ma su fafutikar kawo karshen masu tayar kayar baya na ta'addancin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Bincike ya tabbatar da cewa, akwai tsare-tsaren gwamnatin tarayya na fitar da Naira Biliyan 20 wajen tallafawa jami'o'i da ke fadin Najeriya domin habakarsu da bunkasa kamar yadda kasafin kudin bana ya yi tanadi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel