Gobara ta lakume miliyoyi a wata kasuwa, da gangan ne ko azal ce?

Gobara ta lakume miliyoyi a wata kasuwa, da gangan ne ko azal ce?

- Yan kasuwar Wadata dake Makurdi, jihar Benue na kirga asarar da suka tafka

- Gagarumar gobara ta ci kasuwar inda ta lashe kayan miliyoyin kudi

- Sun koka da rashin zuwan yan kwana kwanan jihar da wuri

Gobara ta lakume miliyoyi a wata kasuwa, da gangan ne ko azal ce?
Gobara ta lakume miliyoyi a wata kasuwa, da gangan ne ko azal ce?
Asali: UGC

Yan kasuwar Wadata dake Makurdi, Benue da gobara ta lashe musu dukiyoyi suna kirga asarar su.

Ofishin dillancin labarai ya samo daga majiya mai karfi cewa gobarar ta fara da karfe 1 na daren ranar talata.

Wani yankin yan kasuwan da suka zanta da ofishin dillancin labarai sun koka akan babban rashin da sukayi. Sunce basu san musabbabin barkewar wutar ba.

Philomena Samaka, mai siyar da yaji a kasuwar ta sanar da ofishin dillancin labarai cewa dukkanin shagon ta da kayan siyarwar ta sun kone a ibtila'in.

Mrs Samaka tace da karfe biyun dare aka kirata cewa gobara ta tashi. Amma tayi danasanin zuwa gurin saboda koda taje babu abin da ta iya don tseratar da kayanta.

Wani dan kasuwa, Yakubo Mohammed, mai sana'ar kayan kichin, yace kayan shagon shi zasu kai darajar Naira miliyan 6 da wutar ta lashe.

Mista Yakubu yace duk da sun isa kasuwar da wuri babu abinda suka iya don tseratar da dukiyar su. Yayi kuka da rashin zuwan yan kwana kwanan jihar gurin gobarar da wuri. Yace zuwan yan kwana kwanan da wuri zai iya rage yawan asarar da sukayi.

DUBA WANNAN: PDP na adawa da yadda aka sako sojoji daga barikoki jihoho don 'Operation Rawar Macijiya-Kaasa

Chinidu Eze, mai siyar da kaya, hatsi da kayan kichin, yace shagunan shi uku ne a kasuwar wadanda gobarar duk ta lashe.

Mista Eze yace "Wannan ne karo na biyu da kasuwar tayi gobara."

Yayi kira ga gwamnati dasu tabbatar da sun kare kasuwar daga kara yin gobara nan gaba.

Wani madinki, wanda gobarar bata shafa ba ya koka da asarar da yan'uwan shi sukayi kuma yayi kira ga gwamnati da ta kawo dauki don sassautawa yan kasuwar yawan asarar.

Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa har karfe 7:12 na safe kasuwar na ci da wuta kuma sojin bataliya ta 72 na gurin don kashe gobarar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel