Na koma APC ne bayan hira da Buhari - Tsohon gwamnan PDP

Na koma APC ne bayan hira da Buhari - Tsohon gwamnan PDP

Tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, ya bayyana yadda ya tsinci kansa a jam'iyyar APC bayan ya yi wata hira da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewar yayin hirar ta su, shugaba Buhari ya yi alkawarin fara wa tare da kammala manyan aiyuka a yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo.

A jerin wasu sakonni da ya fitar a shafinsa na Tuwita a jiya, Lahadi, Kalu ya ce Buhari ya cika dukkan alkawuran da ya dauka yayin hirar da suka yi.

Daga cikin aiyukan da tsohon gwamnan ya lissafa shugaba Buhari ya yi akwai babbar hanyar Enugu/Awka/Onitsha, Nitemile zuwa Makurdi.

Na koma APC ne bayan hira da Buhari - Tsohon gwamnan PDP
Buhari da Orji Kalu
Asali: Facebook

Ragowar sune hanyar Okigwe zuwa Arondizogu, da Ohafia zuwa Arochukwu.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar kungiyar gwamnoni Najeriya (NGF) ta ce gwamnonin kasar nan na son biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi amma halin tsananin da tattalin arzikin kasa da jihohi ke ciki ne ke dakatar da su.

Abdulrazaque Bello Barkindo, shugaban sashen yada labarai na NGF, ne ya sanar da hakan yau, Litinin, a Abuja.

DUBA WANNAN: Fashin Offa: Ka daina rawa a kan kabarin mamata - Lai Mohammed ya karyata Sara

Barkindo ya ce matsalar kudi da wasu matsalolin da jihohi da dama ke fuskanta ne ya sa ba zasu iya biyan mafi karancin albashi na N30,000 ba.

Ya ce yin bayani ya zama wajibi saboda kalaman sakataren kungiyar kwadago, Peter Eson, dake bayyana cewar gwamnoni ne basa son yin karin albashin yayin wata hira da aka yi da shi.

Ya kara da cewar batun cewar gwamnoni ne basa son yin karin albashin ba gaskiya bane kuma yunkuri ne na ingiza jama'a.

Kazalika ya bayyana cewar gwamnonin sun yi tayin kara albashi daga N18,000 zuwa N22,000 bayan kwamitin da aka kafa a kan karin albashi ya mika rahotonsa a ranar 6 ga watan Oktoba.

"Gwamnonin sun bayyana cewar zasu iya biyan N22,000 a matsayin mafi karancin albashi, amma hakan ba yana nufin jiha ba zata iya biyan fiye da haka ba. Duk jihar da take da sukuni zata iya biyan fiye da haka, amma N22,000 shine mafi karancin albashi da gwamnonin suka amince da shi bayan doguwar tattaunawa a tsakaninsu," a cewar Barkindo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel