Ganduje zai nada sabbin kwamishinoni 4 a Kano, duba jerin sunayensu

Ganduje zai nada sabbin kwamishinoni 4 a Kano, duba jerin sunayensu

- Gwamnan jihar Kano. Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na cigaba da janye magoya bayan tsohon gwamna Kwankwaso zuwa jamiyyar APC

- A yanzu haka Ganduje ya aike da sunayen wasu tsofin 'yan Kwankwasyya zuwa majalisa domin tantnace su a matsayin sabbin kwamishinoni

- Kazalika, mataimakin gwamnan jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya aike da takardar neman nada Hajiya Amina Inuwa Sa'id a matsayin babbar mai binciken kashe kudade ta jihar Kano

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya aika takardar neman amincewa zuwa majalisar dokoki domin nada wasu mutane 4 a mukaman kwamishina da kuma mutum guda a matsayin babban mai binciken kashe kudaden jihar (Auditor Janar).

Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Kabiru Rurum, ya sanar da hakan yayin zaman majalisar na ranar Alhamis. Kazalika ya bayyana cewar majalisar ta karbi karin wasu wasikun biyu daga ofishin gwamnan.

Ganduje zai nada sabbin kwamishinoni 4 a Kano, duba jerin sunayensu
Ganduje
Asali: Depositphotos

Kamar yadda yake a cikin wasikar, wadanda gwamnan ke son nadawa a matsayin sabbin Kwamishinonin su ne; Injiniya Bashir Yahaya Karaye, Alhaji Mukhtar Ishaq Yakasai, Alhaji Shehu Kura, da Alhaji Muhammad Tahir da aka fi sani da 'Baba Impossible'.

DUBA WANNAN: 2019: Tsohon janar a rundunar soji ya shawarci masu takara da Buhari

Rurum ya karanta wasika ta biyu daga ofishin mataimakin gwamna, Nasiru Gawuna, dake neman amincewar majalisar domin nada Hajiya Amina Inuwa Sa'id a matsayin babbar mai binciken kashe kudade ta jihar Kano.

"Mun samu wata wasikar dake neman amincewar majalisa domin kafa wata makarantar karatun lafiya da wata cibiyar inganta lafiyar al'umma," a cewar Rurum.

Shugaban majalisar ya bukaci mutanen da gwamnan ya aike da sunayensu da su bayyana a zauren majalisar domin tantancewa a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel