Fadar shugaban kasa ta shiga cakwakiya a kan kauyen Zamfara da aka kashe mutane 25

Fadar shugaban kasa ta shiga cakwakiya a kan kauyen Zamfara da aka kashe mutane 25

Fadar shugaban kasa ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda 'yan ta'adda suka kashe a wasu garuruwa na jihar Zamfara a farkon wannan makon sai dai tayi kuskuren garin da maharan suka fi kashe mutane a wannan shekarar.

A sakon da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ya ce "gwamnati tayi tir da kashe-kashen 'yan Najeriya da akayi a garin Birnin Magaji da ke karamar hukumar Tsafe da garin Magami a mazabar Faru da ke karamar hukumar Maradun na jihar na Zamfara."

Sai dai kuskuren shine Birnin Magaji karamar hukuma ce mai zaman kanta duk da cewa tana cikin Birnin Magaji ne. Hakan na nufin cewa Birnin Magaji ba gari bane a karkashin karamar hukumar Tsafe kamar yadda fadar shugban kasa ta fadawa al'umma duk da cewa 'yan bindigan sun kai hare-hare a Tsafen.

Fadar shugaban kasa ta shiga cakwakiya a kan kauyen Zamfara da aka kashe mutane 25

Fadar shugaban kasa ta shiga cakwakiya a kan kauyen Zamfara da aka kashe mutane 25
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya

A kalla mutane 25 ne aka kashe a hare-haren da 'yan ta'adda suka kai a karamar hukumar Birnin Magaji tsakanin ranar 19 zuwa 20 ga watan Disamba. An kuma sake kai hari a karamar hukumar Maradun kwanaki biyu bayan harin Birnin Magaji inda aka kashe mutane da dama.

Kazalika, an kuma kashe mutane 18 a karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara a cikin kwanakin.

Wannan kuskuren ya sanya wasu masu nazarin al'amuran yau kullum zargin cewa shugaban kasar bai san garuruwan da akayi kashe-kashen ba duk da cewa ya dauki kwanaki kafin ya fitar da sakon ta'aziyyar.

"Abin kunya ne da damuwa ganin cewa shugaban kasa bai san garin da aka yiwa al'umma kisan kiyashi ba," inji wani mai sharhi kan harkokin siyasa, Sola Olubanjo. "Kamar dai fadar shugaban kasa ta tsara sakonin ta'aziyya ne da za ta rika fitarwa bayan an kai hari."

"Idan shugaban kasa bai san Birnin Magaji ba a yanzu, anya ya ko san halin rashin tsaro da al'ummar kasar nan ke ciki," inji Sola.

Premium Times tayi kokarin tuntubar Garba Shehu domin ji ta bakinsa amma ba a same shi a waya ba a ranakun Alhamis da Juma'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel